Gwamnan Jihar Benue Ya Yi Martani Mai Zafi Bayan Yan Bindiga Sun Sace Kwamishina a Jiharsa
- Gwamna Hyacinth Alia, ya yi Allah wadai da aika-aikar da ƴan bindiga suka tafka na sace kwamishina da tsohon shugaban ƙaramar hukuma jihar Benue
- Gwamnan ya bayyana satar manyan ƴan siyasan guda biyu a matsayin aikin jahilci wanda ba za a amince da shi ba
- Gwamna Alia ya kuma umarci jami'an tsaro da su gaggauta kuɓutar da mutanen biyu cikin ƙoshin lafiya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi kakkausar suka kan sace kwamishinan watsa labarai, al'adu da yawon bude ido na jihar, Mista Matthew Abo da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ukum, Mr Iorwashima Erukaa.
Jaridar Channels tv ta kawo rahoto cewa gwamnan ya yi wannan kakkausar sukar ne a ranar Litinin, 25 ga watan Satumba.
Babban Sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Benue, Tersoo Kula, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce wasu ƴan bindiga ne suka yi garkuwa da Abo a gidansa da ke Sankara da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Lahadi, yayin da aka yi garkuwa da Erukaa ranar Asabar, 23 ga watan Satumba.
Sanarwar ta bayyana cewa tun bayan sace mutane biyu, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan Erukaa amma har yanzu ba su tuntubi iyalan Abo ba, rahoton The Telegraph ya tabbatar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Gwamna Hyacinth Alia ya samu labari mara daɗi na sace Mista Matthew Abo, kwamishinan watsa labarai, al'adu da yawon bude ido, da kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ukum, Mista Iorwashima Erukaa."
"Yayin da wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da Abo a gidansa da ke Sankara da misalin karfe 8:00 na daren ranar Lahadi, 24 ga Satumba, 2023, wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da Mista Erukaa a ranar Asabar, 23 ga Satumba, 2023."
Wane umarni gwamnan ya ba jami'an tsaro?
Gwamnan wanda ya bayyana lamarin a matsayin aikin jahilci, abun Allah wadai wanda ba za a amince da shi ba, ya umarci hukumomin tsaro da su fara aiki nan take domin ganin an sako mutanen biyu cikin ƙoshin lafiya.
Gwamna Alia ya kuma yi kira ga al'ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, domin gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin jihar ta zauna lafiya.
Jami'an Tsaro Sun Fatattaki Yan Bindiga
A wani labarin kuma, jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar wasu miyagun ƴan bindiga da suka yi yunƙurin sace mutane a jihar Katsina.
Jami'an tsaron sun samun nasarar fatattakar ƴan bindigan ne bayan sun kwashe lokaci mai tsawo suna musayar wuta.
Asali: Legit.ng