Mummunar Gobara Ta Tashi a Kotun Koli Da Ke Birnin Tarayya Abuja

Mummunar Gobara Ta Tashi a Kotun Koli Da Ke Birnin Tarayya Abuja

  • An samu tashin gobara a kotun ƙolin Najeriya da ke a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 25 ga watan Satumban 2023
  • Gobarar wacce ta tashi da sanyin safiya ta shafi wani ɓangare na kotun wanda ke ɗauke da ofisoshin alƙalai uku ciki har da na mai shari'a Ibrahim Saulawa
  • Sai dai, jami'an hukumar kashe gobara da ke a kotun sun samu nasarar kashe gobarar cikin gaggawa kafin ta kai ga yin ɓarna mai yawa

FCT, Abuja - Gobara ta tashi a wani sashe na kotun ƙoli da ke birnin tarayya Abuja da sanyin safiyar ranar Litinin, 25 ga watan Satumban 2023.

An tabbatar da aukuwar lamarin ne a lokacin shirin safe na gidan talabijin na Arise TV mai suna "The Morning Show".

Gobara ta tashi a kotun koli
Wani bangare na kotun koli ya kama da wuta Hoto: Agu
Asali: Twitter

An tattaro cewa gobarar ta shafi ofisoshin alkalai uku na kotun ƙolin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Benue Ya Fusata Kan Sace Manyan Yan Siyasa a Jiharsa, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene dalilin tashin gobarar?

An tattaro cewa gobarar wacce ta shafi ofisoshi kusan uku ciki har da na mai shari’a Ibrahim Saulawa, ta faru ne a sanadiyyar matsalar wutar lantarki.

Jami’an hukumar kashe gobara da ke a kotun ne suka kashe gobarar, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Mai magana da yawun kotun, Dr. Festus Akande ya tabbatar da aukuwar lamarin, wanda ya bayyana a matsayin ƙaramin lamari.

Akande ya ce tuni ma'aikatan suka daƙile gobarar wacce ta tashi da sanyin safiya.

"Wani ƙaramin lamari ne da wasu daga cikin ma’aikatanmu suka shawo kansa cikin gaggawa da taimakon na'urar kashe gobara." A cewarsa.

Ana samun gobara a ofisoshin gwamnati

Lamarin gobarar dai shi ne na baya-bayan nan da ya shafi ofisoshin gwamnati a Abuja. A watan Mayun 2023, gobara ta ƙone wasu sassa na sansanin sojojin saman Najeriya dake kan titin filin jirgin sama a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Direba Ya Cakawa Jami'in LASTMA Wuka, Ya Yi Tumbur a Bainar Jama'a

A watan Fabrairun 2022, an samu gobara a ginin ma’aikatar kuɗi da ke Abuja. A watan Mayun 2020, gobara ta ƙone wani bangare na ginin hukumar NIPOST a babban birnin tarayya Abuja.

Kamfanin Robobi Ya Kama Da Wuta a Legas

A wani labarin kuma, wata mummunar gobara ta tashi a wani kamfanin sarrafe robobi na Mega Plastics da ke a jihar Legas.

Gobarar wacce ba a gano musabbabin dalilin aukuwarta ba, ta tashi ne a sashen ma'ajiyar kamfanin da ke a unguwar Ilupeju cikin jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng