Ministan kasafin kudi ya yi magana a kan gobarar ofishin babban akawu na kasa
Karamin ministan kasafi da tsare - tsare na kasa, Prince Clem Agba, ya yi magana a kan gobarar da ta tashi a ofishin babban akawu na kasa inda ake zargin ta tafka barna a ginin ofishin da ake kira da 'rumbun ajiye kudin kasa (treasury house)'.
"Mu na wani taro na wasu ministoci da mambobin majalisa lokacin da labarin tashin gobarar ya same mu, kuma nan da nan na nemi a yi min uzuri don na garzayo na ga halin da ake ciki.
"Lokacin da na iso tuni jami'an hukumar kashe gobara na tarayya tare da hadin gwuiwar jami'an kashe gobara daga babbban bankin kasa (CBN) da jami'an kashe gobara na FCT da na wasu kamfanoni sun kashe wutar da ke ci.
"Gobarar ta fara ne da misalin karfe 10 na safe, wutar ta tashi ne sakamakon haduwar wayar wutar lantarki a wurin kunna na'urar sanyaya daki da wani jami'i ya kunna a hawa na hudu na benen gini.
"Mun duba sashen adana bayanai mun ga gobarar ba ta shafi bangaren ba, duk da ta taba dakin wasu na'urori da ke sanyaya wurin adana bayananmu.
DUBA WANNAN: Yadda za mu cigaba da ciyar da dalibai duk da an rufe makarantu - Ministar jin dadi da walwala
"Ba mu kammala bincike da sanin barnar da gobarar ta yi ba, amma zan iya tabbatar muku da cewa duk bayana da suka shafi harkokin kudi da hada-hadarsu, basu samu wata matsala ba," a cewar ministan yayin ganawarsa da manema labarai jim kadan bayan an kashe gobarar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng