Gwamna Kefas Na Jihar Taraba Ya Amince A Biyan Masu Bautar Kasa Naira Dubu 245 A Jihar
- Masu bautar kasa a jihar Taraba za su kwashi garabasa yayin da Gwamna Kefas ya amince da biyan makudan kudade
- Gwamna Agbu Kefas shi ya bayyana haka a jiya Lahadi 24 ga watan Satumba a shafinsa na Twitter
- Ya ce gwamnatinsa ta amince da biyan Naira dubu 50 na lafiya da dubu 25 na wurin zama sai kuma dubu 10 ko wane wata na tallafi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Taraba – Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya amince da biyan matasa masu bautar kasa alawus na Naira dubu 245 da aka tura makarantu.
Kwamishinar yada labarai a jihar, Zainab Usman ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa a jiya Lahadi 24 ga watan Satumba, Legit ta tattaro.
Ya yanayin karin alawus na NYSC ya ke a Taraba?
Ahaf: Tinubu ya dawo da 'yan Najeriya baya cikin bakin talauci sadda ya cire tallafin mai, malamin jami'a
Zainab ta ce daga cikin alawus din dubu 50 na kula da lafiya ce sai kuma dubu 25 na wurin zama da kuma dubu 10 tallafawa daga jiha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce gwamnan ya amince da hakan ne bayan ya tabbatar da ilimi kyauta a jihar wanda hakan ya jawo komawar dalibai da dama makaranta.
Ta ce:
“Yawan karuwar shiga makarantu musamman bayan kaddamar da shirin bayar da ilimi kyauta ya saka gwamnan daukar wannan mataki.
“Saboda kawo sauyi a harkar ilimi Gwamna Kefas ya amince da karin Naira dubu 10 a kowa ne wata.
“Sannan za a biya Naira dubu 50 na lokaci daya don kula da lafiyarsu da kuma Naira dubu 25 na wurin zama.”
Wane alkawari aka yi wa matasan NYSC?
Zainab ta kara da cewa duk wasu matasa masu bautar kasa da su ka bambance kansu wurin yin aiki tukuru za a ba su aiki a jihar.
Rahotanni sun tattaro cewa an samu karuwar komawar dalibai makaranta a jihar saboda bayar da ilimi kyauta da Gwamna Kefas ya yi.
Wani malami mai suna, Isa Mohammed ya ce a makarantarsu ta Salihu Dogo ta samu karin dalibai kusan 300 a satin da ya gabata.
Zulum ya bai wa 'yan bautar kasa miliyan 36 na rage radadi
A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya ware Naira miliyan 36 don rabawa 'yan bautar kasa 1,215 a jihar.
Zulum ya sanar da hakan ne yayin kai ziyara sansanin horas da matasan a Maiduguri babban birnin jihar.
Asali: Legit.ng