Tsohuwar Matar Obasanjo Ta Aike Masa Da Martani Mai Zafi

Tsohuwar Matar Obasanjo Ta Aike Masa Da Martani Mai Zafi

  • Taiwo Martins ta hasala kan kalaman da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi a kanta bayan ta nemar masa afuwa
  • Tsohon shugaban ƙasar dai ya yi mata kaca-kaca inda ya bayyana ta a matsayin mayaudariya wacce ta ke nuna kanta a matsayin matarsa
  • Sai dai, a martanin da ta yi wa tsohon shugaban ƙasar, Taiwo ta bayyana shi a matsayin babban mayaudari wanda ya assasa matsalolin ƙasar nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Matar tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, Taiwo Martins, ta bayyana shi a matsayin babbar matsalar Najeriya kuma babban mayaudarin da babu kamarsa, cewar rahoton The Nation.

A makon da ya gabata ne dai Obasanjo ya yi watsi da ita bayan ta roki ‘yan Najeriya da su yafe masa saboda yadda ya wulakanta sarakunan gargajiya a garin Iseyin na jihar Oyo.

Kara karanta wannan

"Dalilin Da Yasa Na Shiga Siyasa": Obasanjo Ya Magantu Ya Fadi Hanya 1 Da Za a Magance Juyin Mulki a Afirika

Tsohuwar matar Obasanjo ta yi masa wankin babban bargo
Taiwo Obasanjo ta bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin babban mayaudari Hoto: Facebook
Asali: UGC

Sai dai, a martanin da Taiwo ta yi a cikin wata sanarwa ta bayyana tsohon shugaban ƙasan a matsayin wanda ya yi amanna cewa yana da ƙarfin da ba za a iya kalubalantarsa ​​ba kuma wanda ba ya ɗaukar gyara ko kaɗan, rahoton PM News ya tabbatar.

Taiwo ta caccaki Obasanjo

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina so duniya ta sani cewa Cif Olusegun Obasanjo shi ne babban mayaudari, maƙaryaci, mayaudari wanda a yanzu yake ganin kansa kamar wani ubangiji da girman da yake ganin ba za a iya kalubalantarsa ​​ba."
"Da zarar Obasanjo ya ga ba za ka amince da abin da yake so ba ɗari bisa ɗari, sai ya mayar da kai maƙiyinsa inda zai yi duk mai yiwuwa domin ya lalata ka. Zai yi amfani da duk ƙarfinsa wajen lalata duk wanda ya ba shi shawara mai kyau."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ƙara Tankaɗe da Rairaya, Ya Kori Wasu Manyan Ma'aikata

"Ina ƙara maimaitawa cewa kai ne babban mayaudari wanda kamar shaiɗan ka ke yawo a matsayin maganin matsalolin da ka ƙirƙiro mana a nan Najeriya da nahiyar Afirika."
"Kai ne ainihin matsalar da ke damun Najeriya, al’ummar Najeriya baki ɗaya."

Obasanjo Ya Bayyana Dalilin Shigarsa Siyasa

A wani labarin kuma, tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi tsokaci kan dalilan da suka sanya shi ya shiga cikin siyasa.

Obasanjo ya bayyana cewa shigarsa siyasa tsautsayi ne inda ya ƙara da cewa son da yake yi na ganin yana hidimtawa jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng