“Ban San Namiji Ba”: Budurwa Yar Shekaru 36 Ta Sha Alwashin Kare Kanta Har Dakin Miji

“Ban San Namiji Ba”: Budurwa Yar Shekaru 36 Ta Sha Alwashin Kare Kanta Har Dakin Miji

  • Shawarar da Sonali Chandra ta yanke na kauracewa tarayya da 'da namiji har sai ta yi aure ya janyo mata hasarar masoya da dama
  • Matashiyar mai shekaru 36 a duniya ta ce yawancin maza na tserewa da zaran sun ji cewa ita din mai tsarki ce kuma bata da niyar bayar da kanta ga wani namiji har sun yi aure
  • Abun mamaki shine akwai wasu da ke aika mata sakonni suna ganin sun mallaki abun da zai sa ta sauya matsayinta

Har yanzu da take shekaru 36 a duniya, matashiyar nan mai rawa da wasan barkwanci a birnin New York, Sonali Chandra, bata san 'da namiji ba.

Sai dai kuma, hakan ya janyo mata hasarar masoya da dama kamar yadda ta bayyana cewa maza basu son irin matan nan a yanzu.

Kara karanta wannan

"Ta Mato": Bidiyon Yadda Samari 3 Suka Durkusa Har Kasa Don Nemawa Abokinsu Lambar Budurwa Ya Girgiza Intanet

Matashiya yar shekaru 36 tace har yanzu bata san 'da namiji ba
“Ban San Namiji Ba”: Budurwa Yar Shekaru 36 Ta Sha Alwashin Kare Kanta Har Dakin Miji Hoto: News.com.au.
Asali: UGC

Sonali na so ta tsira da mutuncinta na 'ya mace

Ta fada ma News.com.au cewa niyanta shi ne ta ci gaba da kasancewa cikin tsarki har sai ta yi aure, lamarin da ke sa masu neman aurenta tserewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sonali ta kara da cewar dagewar da ta yi na kauracewa badala har sai ta yi aure da kuma rashin gogewa a harkar daya dakin shine babban kalubalenta.

Matar wacce ta kasance ruwa biyu wato yar Indiya da Amurka ta alakanta wannan tsattsauran ra'ayi nata da yadda aka tayar da ita kuma saboda haka tana kallon tarayyar mace da namiji a matsayin wani abu na musamman.

Ta ce:

"Karo na farko da na fada ma saurayi cewa har yanzu ni budurwa ce ya kasance lokacin da nake da shekaru 26 a duniya. Saurayin wanda shine mutum na farko da na fara sumbata, wato dai saurayina na farko, ya kadu."

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Aikewa Saurayi Sakon Rabuwa Bayan Ya Siya Mata Sabon iphone 15, Ya Zauce

Mutane na yi mata kallon yar madigo

Ta tuna yadda saurayinta na farko ya cika da mamaki lokacin da ta sanar da shi sharuddanta, wanda daga baya ya tambayeta ko tana shirin zama a haka muddin rayuwarta.

"Na ce, saurara dan saurayi, ina bukatar zobe, ka sani? Ya bace mun da gani bayan watanni shida a ranar zagayowar haihuwata," ta kara da cewa.

Hakan ne ya ci gaba da kasancewa a gareta domin dai wasu masoyanta biyu sun rabu da Sonali bayan sun gano cewa ba za ta yi harka ba kafin aure.

Ta kara da cewar wasu kuma sun rufe da cewar bata ra'ayin zama idan har bata muradin hada gado da su.

Maza na son mallakar Sonali

Abun mamaki, shawararta na sanar da duniya halin da take ciki ya janyo mata farin jinin maza da ke son sace zuciyarta.

"Sun san cewa ni mai tsarki ce, abu ne da suke son mallaka," ta bayyana.

Kara karanta wannan

Mata Ta Bayyana Yadda Ta Samu Juna Biyu Daga Cewa A Mata Tausa, Bidiyon Ya Yadu

Sonali ta bayyana cewa duk da cewar ta rasa sa'a a so saboda matsayinta, bata danasani kan alwashin da ta sha.

Saboda haka, ta ce tana fatan jama'a da yan uwanta za su daina matsa mata kan cewa kawai ta aikata shi.

"Sai kace takobi": Bidiyon takalman wani mutum ya girgiza intanet

A wani labarin, wani mutum ya yi fice sosai a dandalin TikTok bayan wani bidiyo ya hasko dogayen takalman da ya sanya a kafafunsa.

A cikin bidiyon wanda @omotonso_1 ya wallafa, an gano mutumin cikin mutane a wani wuri da ya yi kama da mashaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng