Mutum 3 Sun Rasu a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Imo
- Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Imo ya salwantar da rayukan direbobi biyu da fasinja ɗaya
- Hatsarin motar wanda ya auku a kan hanyar Owerri/Aba ya ritsa da wata motar bas mai ɗauke da fasinjoji 18
- Kwamandan hukumar FRSC ta jihar ta tabbatar da aukuwar harin inda ta ce ragowar fasinjojin da suka samu raunika an ba su kulawa a asibiti
Jihar Imo - Rahotanni sun bayyana cewa mutane uku ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Owerri/Aba a jihar Imo.
Jaridar TheCable ta ce Angela Fagbenide, kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta kasa (FRSC) a jihar Imo, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis, 21 ga watan Satumban 2023.
Yadda hatsarin ya auku
Fagbenide ta bayyana cewa motar da hatsarin ya ritsa da ita wata motar bas ce mai kujeru 18 wacce ke cike da fasinjoji inda ta taso daga Aba zuwa Owerri.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ta ce motar bas ɗin na dauke da kaya, inda ta ƙara da cewa direbobin motocin biyu ciki har da wata fasinja mace sun mutu, cewar rahoton The Sun.
Ta kuma bayyana cewa sauran fasinjojin sun samu raunuka a yayin hatsarin.
"Kimanin mutane bakwai da hatsarin ya ritsa da su da aka kwantar a asibitin IAWA da ke ƙaramar hukumar Ngor-Okpala, an yi musu magani kuma an sallame su." A cewarta.
"An kuma gano wasu kayayyaki da suka hada da kudi a wurin da hatsarin ya auku. Za a miƙa su a hannun ƴan uwansu a yau ɗin nan."
Ta kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da rahotannin da ke cewa fasinjoji 18 ne suka rasa rayukansu a hatsarin.
Wani ganau ba jiyau ba ya ce motar bas ɗin da hatsarin ya rutsa da ita ta wuce motarsa a mahadar Olakwu, inda ya ƙara da cewa hatarin ya yi muni.
Direban Babbar Mota Ya Murkushe Jami'in FRSC
A wani labarin kuma, wani direban babbar mota ya murƙushe wani jami'in hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar Legas.
shaidun gani da ido sun bayyana cewa jami'in, an matse shi ne a jikin wasu manyan motoci guda biyu har sai da ya mutu.
Asali: Legit.ng