Sama Da Mafarauta 1,000 Ne Aka Shigar Cikin Yaki Da Ta'addanci a Bauchi
- Mafarauta sun shiyar bayar da gudunmawarsu domin kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci a jihar ta yankin Arewa maso Gabas
- Sama da mafarauta 1,000 ne aka tattaro domin shiga cikin yaƙin da ake yi na ganin cewa an kakkaɓe ƴan bindiga daga jihar
- A cikin ƴan kwanakin ayyukan ƴan bindiga na masu garkuwa da mutane sun ƙaru a jihar wanda hakan ya sanya tsoro a zukatan jama'a
Jihar Bauchi - Sama da mafarauta 1,000 aka tattaro domin shiga cikin yaƙi da ayyukan ta'addanci da fatattakar ƴan ta'adda a maɓoyarsu a dazukan da ke yankin Lame cikin ƙananan hukumomin Gumau da Toro na jihar Bauchi.
A yayin wata tattauna da gidan talbijin na Trust Tv, Hakimin Lame wanda kuma shi ne Sarkin yaƙin Bauchi, Aliyu Yakubu Lame, ya roƙi hakiman yankin da su ba da kulawa ta musamman kan yaƙi da masu garkuwa da mutane da ƴan bindigan da suka yi wa yankin ƙawanya.
Gwamnati na bayar da gudunmawa
Sarkin wanda ya ce gwamnatin jihar da jami’an tsaro sun taimaka wajen yaki da ‘yan bindiga a jihar, ya kuma buƙaci jama'ar yankin da su kasance cikin shirin bayar da gudunmawarsu wajen korar ƴan ta'addan tare da sanya idanu kan baƙin fuskoki yankunansu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Su ƴan bindigan ba su zaune ne a cikin ƙauyuka, suna zaune ne a saman duwatsu da cikin dazuzzuka. Shigar da mafarauta a yaƙin da ake yi da ƴan bindigan ya fara haifar da ɗa mai ido." A cewarsa.
Wane irin hali mutanen yankin ke ciki?
Mazauna wasu daga cikin ƙauyukan yankin na cikin halin ƙaƙa-ni-kayi yayin da al’amuran sace-sacen mutane ke ƙaruwa a cikin ƴan kwanakinnan.
Ƙananan hukumomi bakwai da lamarin ya fi shafa sun haɗa da Toro, Ningi, Alkaleri, Jama’are, Tafawa Balewa, Dass da Bogoro
Hakan ya sanya gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar ya buƙaci rundunar sojin sama da ke Bauchi ta fara aikin sintiri ta sama a dazuzzukan kan maboyar ƴan ta’addan saboda yadda matsalar ke ƙara girmama.
Yan Sanda Sun Cafke Yan Ta'adda 5
A wani labarin kuma jami'an ƴan sanda a jihar Benue sun samu nasarar cafne wasu ƴan ta'adda guda biyar a yankin Sankera na jihar.
Jami'an ƴan sandan sun samu nasarar cafke miyagun ƴan ta'addan ne baya. Sun bo sawunsu zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng