Obasanjo Ya Bayyana Hanyar Da Za a Magance Juyin Mulki a Nahiyar Afirika

Obasanjo Ya Bayyana Hanyar Da Za a Magance Juyin Mulki a Nahiyar Afirika

  • Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban ƙasar Najeriya, bai yi shirin shiga siyasa ba, amma ya shiga ne domin yi wa jama’a hidima
  • Obasanjo ya cigaba da cewa, za a iya kawo ƙarshen juyin mulkin da sojoji ke yi a nahiyar Afirika ne kawai idan shugabanni suka daina yin abin da jama'a suka gaji da shi
  • A cewar tsohon shugaban ƙasar ya kamata matasa su yi kokarin shiga siyasa domin yi wa jama'a hidima

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abeokuta, Ogun – Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya tsinci kansa ne kawai a siyasa amma ba ta a cikin tsarinsa.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wasu matasa a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar Africa for Africa Youth Initiative (A4A), a daƙin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL) da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Fusata, Ya Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Matarsa Da Ta Roki Sarakuna a Madadinsa

Obasanjo ya bayyana dalilin da ya sanya ya shiga siyasa
Obasanjo ya bayyana yadda za a magance aukuwar juyin mulki a nahiyar Afirika Hoto: Olusegun Obasanjo
Asali: Twitter

Obasanjo ya bayyana dalilin da ya sa dole matasa su shiga siyasa

A cewar tsohon shugaban na Najeriya, ya shiga siyasa ne saboda irin soyayyar da yake yi wa al'ummarsa da son kawo cigaban al'umma, rahoton Vanguard ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga nan ya yi kira ga matasa da su tabbatar sun shiga siyasa domin hidimtawa jama'a.

A kalamansa:

"Siyasa hidimtawa ce. Dole ne ka hidimta. Babu wanda ya yi girma ko ƙanƙanta ko matalauci da ba zai iya yin hidima ba. Lokacin da muka fara hidimtawa mai inganci, to za mu samu ingantaccen shugabanci."

Obasanjo ya bayyana dalilin yin juyin mulki a Afirika

Daga nan sai tsohon shugaban ya yi tsokaci game da juyin mulkin da sojoji suke yi a nahiyar Afirika cikin ƴan kwanakin nan, inda ya ƙara da cewa ya kamata shugabanni a kowane mataki su guji duk wani yanayi da zai kai ga dawowar sojoji a nahiyar.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Na Kusa da Atiku Abubakar Ya Tona Asirin Gwamnatin Shugaba Tinubu Kan Abu 1 Tal

Ya yi nuni da cewa juyin mulkin da ake samu a ƙasashen baƙar fata, ya nuna cewa mutane sun gaji da wasu abubuwan da ke faruwa a ƙasashensu kuma suna neman waɗanda za su ƙwato musu ƴanci.

"Juyin mulkin da sojoji suke yi a nahiyar Afirika ya nuna cewa mutane sun gaji da wasu abubuwa da ke faruwa a kasashensu kuma suna neman waɗanda za su ƙwato musu ƴanci." A cewarsa.

Obasanjo Ya Fusata Kan Tsohuwar Matarsa

A wani labarin kuma, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, ya fusata kan neman yafiyar sarakunan Yarabawa da tsohuwar matarsa ta yi a madadinsa.

Taiwo Obasanjo dai ta nemi sarakunan na Yarabawa a jihar Oyo da su yafewa tsohon shugaban ƙasan bayan ya umarce su da su tashi tsaye a wajen wani taro kamar ƙananan yara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng