An Kwancewa Obasanjo Rawanin Balogun Na Owu Da Wasu Sarautun

An Kwancewa Obasanjo Rawanin Balogun Na Owu Da Wasu Sarautun

  • An daina kallon tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin Balogun na masarautar Owu a Abeokuta, jihar Ogun
  • Bayan ya ki bayar da hakuri cikin kwanaki uku, majalisar Yarbawa ta duniya ta janye sarauta da tsohon shugaban kasar ke da su
  • Kungiyar ta kuma bayyana cewa daga yanzu ba za a dunga kiransa da duk wasu sarautun da sauran sarakunan Yarbawa suka nada masa ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja Majalisar Yarbawa ta duniya ta daina daukar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin Balogun na masarautar Owu da ke Abeokuta, jihar Ogun.

Ci gaban na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka aikewa Legit a ranar Talata, 19 ga watan Satumba dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Aare Oba Oladotun Hassan Esq.

Obasanjo da sarakunan yarbawa
Da Dumi-Duminsa: An Janye Duk Wasu Sarauta Obasanjo Yake Da Su a Kasar Yarbawa Hoto: @Oolusegun_obj/@tvcnewsng
Asali: Twitter

Hakan na zuwa ne sakamakon takkadamar da ta faru tsakanin tsohon shugaban kasar da wasu sarakunan Yarbawa a wajen kaddamar da wasu ayyukan gwamnati a Iseyin, jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Fusata, Ya Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Matarsa Da Ta Roki Sarakuna a Madadinsa

A cikin wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano Obasanjo cikin fushi yana mai umurtan sarakunan da su tashi su yi gaisuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan lamarin ya ja masa suka daga sauran manyan sarakuna da masu fada aji a kudu maso yamma.

A cikin wata hira ta musamman da Legit, shugaban kungiyar, Aare Hassan, ya bai wa Obasanjo wa’adin kwana uku ya ba da hakuri a taron manema labarai.

Obasanjo ya magantu a kan takkadamarsa da sarakunan Oyo

Obasanjo, wanda ya yi magana kan lamarin, ya ce ya bukaci sarakunan da su tashi tsaye ne saboda sun ki tashi a lokacin da sauran mutane suka tashi don girmama zuwa Gwamna Seyi Makinde.

Kamar yadda yake kunshe a cikin sanarwar da majalisar Yarbawa ta duniya ta yi, an cimma matsayar ne bayan kungiyar ta nemi Obasanjo ya ba da hakuri cikin kwana uku bayan faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Wike Ya Rusa Shahararriyar Kasuwar Kilishi a Abuja, Ya Fadi Dalili

Sai dai kuma, tsohon shugaban kasar ya ki bin wannan umurni domin dai ya ki bayar da hakuri kan abun da ya aikata.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa za a dauki tsauraran matakan shari'a kan tsohon shugaban kasar.

Sun kuma bayyana cewa za du tattara dukkanin "mata yan kasuwa, matasa da shugabanni don ci gaba da tsaftacewa da kuma bin sanarwar mu."

Obasanjo ya fusata, ya dauki mataki mai tsauri kan matarsa da ta ba sarakuna hakuri

A baya mun ji cewa Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya, ya karyata wata Taiwo Obasanjo, wacce ta yi ikirarin cewa ita matar tsohon janar din ce tare da bayar da hakuri a madadinsa kan abun da ya yi wa sarakunan Yarbawa a jihar Oyo.

PM News ta rahoto cewa sojar gonar ta yi kira ga sarakunan da su yafewa tsohon shugaban kasar kan sawa da ya yi suka tashi tsaye da zama kamar wasu yaran makarantar firamare a wajen wani taro a jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng