Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wani Manomi Tare Da Diyarsa a Jihar Kwara
- Miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani manomi tare da ɗiyarsa lokacin da su ke kan hanyar dawowa daga gona a jihar Kwara
- Ƴan bindigan sun sace manomin ne mao suna Kayode Ajayi a yankin Afon na ƙaramar hukumar Asa ta jihar a yammacin ranar Litinin, 18 ga watan Satumban 2023
- Rundunar ƴan sandan jihar ta kakakinta, SP Ajayi Okasanmi, ta tabbatar da aukuwar harin inda ta ce jami'anta na bakin ƙoƙarinsu waje ceto manomin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kwara - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani manomi mai suna Kayode Ajayi, da ƴarsa a jihar Kwara.
Miyagun ƴan bindigan sun sace mutanen ne lokacin da su ke kan hanyarsu ta dawowa daga gona a yankin Afon da ke ƙaramar hukumar Asa a jihar Kwara, cewar rahoton Leadership.
Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a yammacin ranar Litinin, 18 ga watan Satumban 2023.
Babu tabbaci kan cewa ko masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan manomin kan kuɗin fansan da za a ba su, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton a ranar Talata da rana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar harin
Sai dai, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya kuma tabbatar da cewa an samu nasarar ceto ɗiyar manomin, yayin da mahaifinta ke cigaba da zama a hannun masu garkuwa da mutanen.
“Amma ana cigaba da ƙoƙarin ceto mahaifin. Jami'an tsaro na aiki tuƙuru domin tabbatar da hakan." a cewar Okasanmi
Yankin Afon dai ya yi ƙaurin suna wajen yin garkuwa da mutane, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar da yawa daga cikin mutanen da aka sace, tare da biyan miliyoyin kuɗi a matsayin kudin fansa.
Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addini a Enugu
A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun yi awon gaba da wai limamacin cocin Katolika ta Enugu, tare da wasu matafiya mutum shida.
Rev. Fr. M. Okhide na cocin Katolika ta Enugu ya faɗa a hannun ƴan bindigan ne lokacin da yake tafiya akan titin Eke-Affa-Egede a ƙaramar hukumar Udi ta jihar.
Asali: Legit.ng