Manoma da Dama Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Hari Kauyuka 7 a Kebbi da Sokoto
- 'Yan bindiga sun yi ajalin rayukan manoma da yawa yayin sabon harin da suka kai ƙauyukan bodar jihohin Kebbi da Sakkwato
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun tarwatsa kauyuka 7, bisa tilas mutane suka gudu daga gidajensu
- Gwamnatin jihar Kebbi ta tura kayan agaji ga waɗanda suka rasa mahallansu sanadin harin 'yan bindigan dajin
Kebbi, Sokoto - Mutane da yawa mafi yawanci manoma sun rasu yayin da wasu miyagun 'yan bindiga suka kai farmakin rashin imani kan ƙauyuka 7 a bodar jihohin Kebbi da Sokoto.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan bindigan sun halaka mutane da dama kana suka kori wasu masu ɗumbin yawa daga gidajensu a garuruwan da ke arewacin Najeriya.
Kauyukan sun hada da Zawaini Zawaini, Jangargari da Jaja a jihar Kebbi da kuma Karani da wasu uku duk a jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammaci.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun tafka barna yayin harin ciki har da ƙona gidajen jama'a da banka wuta a shagunan 'yan kasuwar ƙauyukan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wane hali mazauna ƙauyukan suka shiga bayan harin?
An tattaro cewa mummunan harin da 'yan bindiga suka kai garuruwan ya tilasta wa mutane barin gidajensu kana suka nemi mafaka a matsayin 'yan gudun hijira a wasu ƙauyuka
Wasu bayanai sun nuna mutane da dama sun zama 'yan gudun hijira a ƙauyen Jarkuka da ke ƙaramar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.
Wane mataki gwamnatin Kebbi ta ɗauka?
An ce Gwamna Nasiru Idris ya bayar da umarnin a raba kayan agaji ga wadanda suka rasa matsugunansu.
Wani jami'an gwamnatin jihar Kebbi ya shaida wa jaridar cewa gwamnan ya tura tawaga ciki har da kwamishinoninsa domin kai kayan tallafi ga waɗanda suka rasa gidajensu.
Kwamishinan harkokin jin ƙai da tallafi, Muhammad Hamidu Jarkuka, da kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na cikin tawagar kai agaji da gwamnan ya tura.
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Fadar Basarake, Sun Kashe Mai Neman Shiga Jami'a
A wani rahoton kuma 'Yan bindiga sun kai farmaki fadar wani basarake, sun ƙona ɗalibi mai neman gurbin shiga jami'a a jihar Osun.
Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sanda reshen jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce tuni aka tura jami'an 'yan sanda zuwa yankin.
Asali: Legit.ng