Gwamnatin Tinubu da NLC Ba Su Cimma Matsaya Ba, Za Su Sake Gana Wa Yau
- Gwamnatin tarayya da ƙungiyar kwadago ta ƙasa NLC sun tashi taro baram-baram ba a cimma komai ba
- Rahoto ya nuna ministan kwadago, Simon Lalong, ya sake shirya gana wa da wakilan ƙungiyar 'yan kasuwa TUC
- NLC ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani kan abinda ta kira tsarukan yaƙar talaka da gwamnati mai ci ta ɓullo da su
FCT Abuja - Jaridar Punch ta rahoto cewa an tashi baram-baram a taron da ya gudana tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC).
Ana tsammanin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Samon Lalong, zai sake sa labule da wakilan ƙungiyar 'yan kasuwa karkashin jagorancin shugaban TUC, Festus Osifo.
Lalong zai gana da wakilan TUC yau Litinin 18 ga watan Satumba, 2023 bayan gaza cimma matsaya tsakanin FG da ƙungiyar NLC.
Tun da fari dai Ministan ya shirya wannan zama ne biyo bayan barazanar da NLC ta yi na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani kan abinda ta kira tsarun yaƙar talakawa da gwamnatin Tinubu ta zo da su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Waɗanda suka halarci ganawar ta yau
Taron ya samu halartar manyan jami'an ma'aikatar ƙwadago, shugaban ƙungiyar NLC na ƙasa, Joe Ajaero, sakataren ƙungiyar, Emmanuel Ugboaja, shugaban ƙungiyar malamai ta Najeriya, Titus Amba, da sauransu.
An tattaro cewa ganawar ta tashi baram-baram domin babu wata hanyar masalaha da aka cimma wa ko wani mataki da kowane ɓangare ya aminta da shi har aka ƙarƙare taron.
Idan baku manta ba NLC ta yi fatali da taron farko wanda gwamnatin tarayya ta shirya amma wakilan ƙungiyar TUC suka samu halarta, Channels tv ta rahoto.
Gwamnatin ta kira taron farkon ne da nufin daƙile yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu da NLC ta ayyana shiga kan wahalhalun da ya biyo bayan tuge tallafin man fetur.
Ondo: Kakakin Majalisa Ya Musanta Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamna
A wani rahoton kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Ondo ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa tana shirin tsige mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa.
Kakakin majalisar, Olamide Oladiji, ya ce labarin ba gaskiya bane kuma ba bu wani shiri da majalisa take yi a ƙarƙashin kasa.
Asali: Legit.ng