Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Gayyaci Direban A-Daidaita-Sahun Da Ya Mayar Da N15m
- Majalisar dokokin jihar Kano ta yaba da halin kirkin da matashin direban a-daidaita-sahu ya yi na mayar da N15m ga mamallakinsu
- Ƴan majalisar sun amince za su bayar da wani kaso na daga cikin albashinsu ga matashin domin karrama shi
- Majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan ɗan majalisar da ke wakiltar Doguwa ya gabatar da kuɗiri kan hakan a gaban majalisar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Ƴan majalisar dokokin jihar Kano sun yi alkawarin bayar da wani kaso na daga cikin albashinsu ga matashin mai a-adaidaita-sahu da ya mayar da N15m na wani ɗan ƙasar Chadi da ya manta su a kekensa.
Hakan dai na zuwa ne bayan wani ƙudiri da ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Doguwa, Alhaji Salisu Muhammad ya gabatar a yayin zaman da shugaban majalisar, Alhaji Isma’il Jibril Falgore ya jagoranta, cewar rahoton Daily Trust.
Matashin mai tuƙa keken a-daidaita-sahun mai suna Auwalu Salisu, wanda yake da shekara 22 a ɗuniya, ya mayar da kuɗin ne har N15m ga ɗan ƙasar Chadin da ya zo sayayya a Kano, bayan ya manta su a kekensa.
A zaman majalisar, Muhammad ya bayyana cewa matashin ya tabbatar da gaskiyarsa ta hanyar mayar da kuɗaɗen ga mamallakinsu, duk kuwa da talaucin da iyayensa ke fama da shi da halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majalisar za ta gayyaci Auwalu
Da yake nasa jawabin, shugaban majalisar, Jibril Falgore ya yi nuni da cewa majalisar za ta gayyato matashin direban a-daidaita-sahun domin gabatar masa da gudunmawarsu.
Dukkanin mambobi 40 na majalisar da ke wakiltar ƙananan hukumomi 44 na Kano sun goyi bayan wannan kudiri tare da yin alkawarin mara wa Auwalu goyon baya don zaburar da shi tare da yin kira ga sauran jama’a da su yi koyi da kyawawan halayensa.
Matashi Auwalu Ya Samu Kyaututtuka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Auwalu Salisu, matashin direban a-daidaita-sahun da ya mayar da N15m da fasinjansa ya manta da su, na cigaba da samun kyuauttuka.
Wasu daga cikin mutanen da suka yaba da halin gaskiyar da ya nuna sun yi masa kyuatuka da suka haɗa da gida, sabuwar keke da gurbin zuwa karatun digiri na biyu.
Asali: Legit.ng