Farashin Mai Na Iya Tashin Gwauron Zabi Saboda Faduwar Darajar Naira A Kasuwanni
- An samu karin farashin danyen mai zuwa Dala 94 wanda shi ne mafi tsada a cikin wannan shekara da mu ke ciki
- Wannan tashin farashin danyen man da kuma faduwar darajar Naira ka iya jawo karin farashin man fetur a Najeriya baki daya
- Kungiyar 'yan kasuwan man a Najeriya ta ce wadannan matsaloli biyu ka iya sa su dole su kara farashin man fetur a kasar ganin yadda al'amura su ke
FCT, Abuja - Akwai alamun karin kudin man fetur bayan tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.
Kungiyar dillalan mai a kasar ita ta bayyana haka a jiya Lahadi 17 ga watan Satumba inda ta ce akwai yiyuwar karin kudin mai saboda karyewar darajar Naira.
Meye zai jawo tashin farashin man fetur?
Rahotanni sun tabbatar cewa a yanzu ana siyar da danyen man a kan Dala 94 kan ko wace ganga, Legit ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wannan bai rasa nasaba da karyewar farashin Naira a kasuwanni wanda ya tilasta siyar man da tsada a kasar.
Dillalan su ka ce tsadar danyen man da kuma darajar Naira na daga cikin dalilai na karin farashin man fetur da kaso 80.
Nawa ake siyar da danyen mai a duniya?
Wannan farashin danyen man kan Dala 94 a ranar Lahadi 17 ga watan Satumba shi ne mafi tsada a wannan shekara, Daily Post ta tattaro.
An fara siyar da danyen man kan Dala 82 yayin da ya sauko Dala 70 a watan Yuni sai kuma Dala 92 a makon da ya gabata.
A ranar Alhamis 14 ga watan Satumba darajar Naira ta fadi inda ake siyar da ita Naira 950 kan ko wace Dala bayan samun karancinta a kasuwanni.
Da Dumi-Dumi: Wutar Lantarki A Najeriya Ta Dawo Bayan Shafe Sa'o'i Babu Ita, An Bayyana Dalilin Hakan
NNPC ta yi asarar Dala 46 saboda sata
A wani labarin, kamfanin mai na NNPC a Najeriya ya bayyana irin asarar da ya yi a cikin kankanin lokaci a kasar.
Kamfanin ya bayyana cewa asarar da ya yi ta kai Dala 46 saboda tsananin satar mai din a Najeriya, musamman a jihohi masu arzikin man fetur.
Wannan na zuwa ne yayin da jama'a ke satar mai din a kullum musamman a Kudancin Najeriya da ke da arzikin man fetur.
Asali: Legit.ng