Gwamnoni sun amince da dokar kulle duk jihohin Najeriya na tsawon kwanaki 14

Gwamnoni sun amince da dokar kulle duk jihohin Najeriya na tsawon kwanaki 14

A ranar Laraba ne dukkan gwamonin jihohin Najeriya 36 su ka amince da kaddamar da dokar kulle kasa baki daya har na tsawon sati biyu domin dakile yaduwar annobar covid-19.

Gwamnonin, a karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), sun cimma wannan matsaya ne bayan sauraron bayanai daga gwamnonin jihohin Lagos, Bauchi, Oyo da Ogun a kan darussan da su ka koya daga yaki da annobar covid-19.

Shugaban kungiyar NGF, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ne ya fitar da wannan sanarwa bayan kammala taron gwamnonin da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar kiran waya mai nuna bidiyo.

A cikin sanarwar, Fayemi ya bayyana cewa babu wanda za a yi wa uzuri sai ma su aiyuka ko bukatu na musamman.

Gwamnoni sun bukaci gwamnatin tarayya ta rage nauyin alhakin duba yaduwar annobar covid-19 daga wuyanta tare da dora shi a wuyan jihohi tunda yanzu ta yadu zuwa jihohi fiye da 25, sannan ta na cigaba da yaduwa.

Gwamnoni sun amince da dokar kulle duk jihohin Najeriya na tsawon kwanaki 14
Gwamnoni sun amince da dokar kulle duk jihohin Najeriya na tsawon kwanaki 14
Asali: Twitter

Kazalika, gwamnonin sun nuna damuwarsu a kan yadda cutar covid-19 ke kama likitoci da sauran ma'aikatan lafiya yayin da su ke aikin ceton rayuwar wadanda aka tabbatar sun ka kamu da kwayar cutar.

DUBA WANNAN: Ganduje ya sasauta dokar kulle a Kano albarkacin watan Ramadan

A saboda haka ne gwamnonin su ka bayyana cewa za su hada gwuiwa da hukumar NCDC wajen bawa ma'aikatan lafiya horo a kan hanyoyin kare kansu yayin da su ke kula da ma su cutar tare da samar mu su wadatattun kayan aiki.

Sun bayyana cewa za su mayar da hankali wajen ganin ana gudanar da bita ga ma'aikatan lafiya domin su san yadda ake amfani da kayan aikin duba ma su cutar covid-19.

Bayan haka, gwamnonin sun amince a kan cewa kowanne yankin kasar nan zai kafa kwamiti da zai kunshi kwamishinonin lafiya na jihohin yankin.

A cewar gwamnonin, kafa kwamitin zai tabbatar da samun musayar muhimman bayanai a kan abubuwan da ke faruwa a kowacce jiha dangane da yaki da annobar covid-19

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng