Jerin Gwamnonin Bankin CBN 13 Da Shugabannin Kasa Da Su Ka Yi Aiki Tare A Najeriya

Jerin Gwamnonin Bankin CBN 13 Da Shugabannin Kasa Da Su Ka Yi Aiki Tare A Najeriya

Tun kirkirarshi a shekarar 1958, Babban Bankin Najeriya, CBN ya samu jagorancin gwamnoni guda 13 da su ka gudanar da harkokin kudade.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Duk wani gwamnan bankin ya samu mukamin ne daga shugaban kasa a wancan lokaci don kawo daidaito a tattalin arziki.

Jerin gwamnonin CBN 13 a Najeriya
Jerin Gwamnonin Bankin CBN 13 A Najeriya. Hoto: @Mr_JAGs/ Central Bank of Nigeria.
Asali: Facebook

Legit ta jero muku sunayen gwamnonin bankin CBN da kuma shugaban da su ka yi aiki tare

1. Roy Pentelow Fenton

Fenton shi me farkon gwamnan bankin CBN wanda dan Burtaniya ne a ranar 24 ga watan Yuli 1958.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnatin mulkin mallaka ne ta nada shi mukamin wanda ya shafe shekaru biyar a kan kujerar.

2. Aliyu Mai-Bornu

Aliyu Mai-Bornu ya gaji kujerar Fenton wanda ya zamo dan Najeriya na farko da ya samu mukamin.

Kara karanta wannan

Shara ta kare a Kano, Abba Gida-Gida ya dauki ma'aikatan tsaftace birni mutum 4500

An nada shi mukamin lokacin gwamnatin Abubakar Tafawa Balewa a ranar 25 ga watan Yuli 1963 zuwa watan Yuni 1967.

3. Clement Nyong Isong

An nada Isong mukamin ne a gwamnatin Janar Yakubu Gowon a ranar 15 ga watan Agusta 1967 a lokacin yakin basasa.

Isong wanda tsohon gwamnan tsohuwar Kuros Ribas ne ya shafe shekaru 8 a kan kujerar.

4. Adamu Chiroma

Chiroma ya kasance gwamnan CBN na hudu daga 1975 zuwa 1977.

Ya rike kujerar a gwamnatocin Murtala Mohammed da Cif Olusegun Obasanjo.

5. Olatunde Olabode Vincent

Vincent masanin tattalin arziki ne da ya rike kujerar daga 1977 zuwa 1982.

Vincent ya rike mukamin ne a gwamnatocin Cif Olusegun Obasanjo da kuma Shehu Shagari.

6. Abdulkadir Ahmed

Shugaban kasa a wancan lokaci, Shehu Shagari ya nada Abdulkadir Ahmed gwamnan CBN a ranar 28 ga watan Yuni 1982.

Ahmed ya fi kowa dadewa a kan kujerar inda ya rike kujerar har na tsawon gwamnatoci guda hudu.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN: Abubuwa 11 da Ya Dace Mutane Su Sani Kan Wanda Tinubu Ya Dauko

Ya rike a lokacin mulkin Shehu Shagari da Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida da kuma Sani Abacha.

7. Paul Agbai Ogwuma

Dakta Paul ya maye gurbin Abdulkadir Ahmed a ranar 1 ga watan Oktoba 1993 lokacin mulkin Janar Sani Abacha.

8. Joseph Oladele Sanusi

Sanusi shi ne gwamnan CBN na takwas a Najeriya wanda Cif Olusegun Obasanjo ya nada shi a ranar 29 ga watan Mayu 1999.

Ya bar kujerar bayan shekaru biyar a ranar 29 ga watan Mayu 2004.

9. Chukwuma Charles Soludo

Soludo ya zama gwamnan CBN a ranar 29 ga watan Mayu 2004 lokacin mulkin Olusegun Obasanjo.

Farfesa Soludo ya yi shekaru biyar a kan kujerar kuma shi ne gwamnan CBN na biyu da ya zama gwamnan jiha.

An rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Anambra a ranar 17 ga watan Maris 2022.

10. Sanusi Lamido Sanusi

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara Sakawa El-Rufai Bayan Nada Yaronshi Shirgegen Mukami, Bayanai Sun Fito

Marigayi Musa Yar'adua ya nada Sunusi gwamnan CBN a ranar 3 ga watan Yuni 2009.

Sunusi shi ya fara kawo tsarin BVN kafin Goodluck Jonathan ya kore shi a ranar 20 ga watan Faburairu 2014.

11. Sarah Alade

Sarah Alade ta kasance mace ta farko da ya rike mukamin a matsayin gwamnan bankin na rikon kwarya bayan korar Sunusi Lamido.

12. Godwin Emefiele

An nada Godwin Emefiele gwamnan CBN a ranar 3 ga watan Yuni 2014 a mulkin Goodluck Jonathan.

Emefiele ya ci gaba da rike mukamin har a mulkin Muhammadu Buhari kafin Shugaba Tinubu ya dakatar da shi a ranar 9 ga watan Yuni 2023.

13. Olayemi Cardoso

Shugaba Tinubu ya nada Olayemi Cardoso gwamnan CBN a ranar 15 ga watan Satumba 2023.

Tinubu ya nada Cardoso gwamnan CBN

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya nada Michael Cardoso a matsayin gwamnan CBN.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 12 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Mukaddashin Shugaban Hukumar FIRS

Wannan na zuwa ne watanni uku bayan Shugaba ya dakatar da Godwin Emefiele a watan Yuni na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.