Matashin Mai A-Daidaita-Sahu Ya Samu Kyaututtuka Bayan Ya Mayar Da N15m
- Matashin mai a-daidaita-sahu da ya mayar da N15m da wani fasinjansa ya manta a kekensa na cigaba da samun yabo da kyaututtuka
- Matashin ya zama abun magana ne a yanar gizo bayan ya nuna tsantsar gaskiyarsa ta hanyar mayar da kuɗin ga mamallakinsu
- Mutane da dama sun yaba da namijin ƙoƙarin da ya yi na mayar da kuɗin, inda wasu daga ciki suka yi masa kyaututtuka na musamman
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Matashin direban a daidaita sahu, mai suna Auwalu Salisu, da ya mayar da N15m da fasinjansa ya bari ya kekensa na cigaba da samun goma ta arziƙi.
A cikin ƴan kwanakin nan ne dai labarin matashin ya karaɗe ko ina kan wannan namijin ƙoƙarin da ya yi na mayar da kuɗaɗen ga mamallakinsu ɗan ƙasar Chadi.
Matashin Mai A-Daidaita-Sahu, Ya Mayar Da Makudan Kudin Da Aka Manta a Kekensa, Ya Samu Babbar Kyauta
Mutumin wanda ya zo daga ƙasar Chadi domin yin sayayya a Kano, ya manta kuɗaɗen ne a keken matashin.
Bayan ya mayar masa da kuɗaɗen, mutumin ya ɗauki N400k ya ba shi kyauta sannan ya godewa iyayensa bisa tarbiyya ta gari da suka ba yaron na su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jama'a sun haɗa masa sha tara ta arziƙi
Biyo bayan bayyanar wannan halin kirkin da matashin ya nuna, mutane da dama sun yaba masa kan wannan namijin ƙoƙarin da ya yi.
Domin yaba wa da abin da matashin ya yi, wasu mutane sun yi masa kyaututttuka masu yawa.
Kamar yadda @AhmedGanga ya sanya a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), matashin ya samu kyauttuka kamar haka:
1. Hajiya Mariya ta ba shi kyautar gida.
2. Sarkin Hausawan Chadi ya ba shi kyautar kudi kwatankwacin sabon keke Napep.
3. Alh Yahaya Singer ya ba iyayensa kyautar abinci iri-iri wanda zai yi musu aƙalla shekara guda.
4. Wani wanda ba a bayyana sunansa ba ya yi alkawarin ba shi tallafin karatu na digiri na biyu.
Dattijon Da Aka Yi Wa Kyautar Kudi Ys Fashe Da Kuka
A wani labarin kuma, wsni dattijo ya zubar da hawaye bayan wani matashi ya yi masa kyautar kuɗi.
Dattijon wanda tsohpn soja ne ya haɗu da matashin ne bayan ya je banki domin jin ba'asi kan kuɗin fanshonsa tun na shekarar 2002.
Asali: Legit.ng