Jerin Jihohin Najeriya Guda 10 Da Su Ka Fi Tsadar Rayuwa Da Tashin Farashin Kaya

Jerin Jihohin Najeriya Guda 10 Da Su Ka Fi Tsadar Rayuwa Da Tashin Farashin Kaya

  • Akalla akwai jihohi 10 a Najeriya da su ka fi tsadar rayuwa musamman na tashin farashin kayayyaki
  • Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da sabon rahoto a Najeriya
  • Rahoton ya tabbatar da cewa Kogi da Legas da kuma Ribas a matsayin wadanda su ka fi fuskantar tsadar rayuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da sabon farashin kayayyaki inda ta ce jihohin Kogi da Legas da Ribas sun fi tsadar rayuwa.

Wannan kididdiga ya shafi watan Agusta na shekarar 2023 inda jihar Kogi ta fi ko wace tashin farashin kayyaki a Najeriya da kaso 31.50, Legit ta tattaro.

Jihohi 10 a Najeriya da su ka fi tsadar rayuwa na tashin farashin kaya
Jerin Jihohin Najeriya 10 Da Su Ka Fi Tsadar Rayuwa. Hoto: Bloomberg / Contributor.
Asali: Getty Images

Wasu jihohi ne su ka fi tsadar rayuwa?

Mai bi mata ita ce jihar Legas da kaso 29.17 sai kuma jihar Ribas a Kudancin Najeriya da kason da ya kai 29.06.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Innalillahi, Bene Mai Hawa 20 Ya Rushe Kan Jama'a a Babban Birnin Jihar PDP

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya ta samu tashin farashin kayan fiye da 20.91 yayin da Borno ke da kaso 21.77 sai kuma jihar Nasarawa da kaso 22.06.

A cikin wata, jihohin Kwara da Osun da Kogi sun fi kowa samun tashin farashin kayayyaki a watan Agusta yayin da Sokoto da Borno da Ogun su ka samu mafi karanci.

A bangaren abinci ma, Kogi ta fi ko wace jiha samun tashin farashin da kaso 38.84 sai kuma jihar Legas ke biye mata da kaso 36.04 sai jihar Kwara da kaso 35.33.

Wasu jihohi ne su ka fi dama-dama a tsadar rayuwa?

Jihar Sokoto ta samu kaso 20 na tashin farashin abinci yayin da Nasarawa ta samu kaso 24.35 da kuma Jigawa da kaso 24.53 a ko wace shekara.

Kara karanta wannan

Tiriliyan 87 Na Bashin Najeriya, Tinubu Ya Gaza Tabuka Komai, An Bayyana Wadanda Ke Bin Kasar Bashi

Punch ta tattaro cewa jihohin Ribas da Kwara da Kogi a ko wane wata sun fi kowa samun tashin farashin abinci yayin da jihohin Sokoto da Neja da kuma birnin Abuja su ka fi karancin tashin farashin abincin.

Hukumar NBS ta bayyana irin kalar abincin da su ka fi tsada kamar su kifi da kayan ganye da dankali da nama da kayan marmari da kuma biredi, Daily Post ta tattaro.

Rashin Aikin Ya Ragu A Najeriya Da Kaso 4.1 A Farkon 2023

A wani labarin, Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce rashin aikin yi a Najeriya ya ragu da kashi 4.1 cikin dari a farkon wannan shekara ta 2023.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta fitar da sanarwar cewa rashin aikin yi din ya kai 5.3 a karshen shekarar 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.