Hawaye Yayin da Wani Harsashi Ya Halaka Dalibar UNIZIK a Jihar Anambra

Hawaye Yayin da Wani Harsashi Ya Halaka Dalibar UNIZIK a Jihar Anambra

  • Wata ɗaliba da ke matakin shekarar farko a jami'ar Nnamdi Azikiwe University (UNIZIK) Awka, ta rasa rayuwarta ba zato ba tsammani
  • Ɗalibar ta mutu sakamakon wani harsashi da same ta wanda ake zargin 'yan kungiyoyin asiri ne suka harbo shi da yammacin ranar Alhamis
  • Rahoto ya nuna cewa wannan mummunan lamarin ya auku ne a mahaɗar titunan Miracle a Awka, babban birnin jihar Anambra

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Anambra - Wani harsashi da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka harbo shi ya kashe wata daliba mai suna, Uche Joevita Chigozirim, da ke karatun a jami’ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK).

Rahotanni sun bayyana cewa ɗalibar tana ajin farko (100 Level) a jami'ar UNIZIK da ke Awka a jihar Anambra kuma ta rasa rayuwarta ba zato ba tsammani.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Mummunan Ibtila'i Ya Laƙume Rayukan Mata 5 a Cikin Mota

Jami'ar UNIZIK da ke Awka, jihar Anambra.
Hawaye Yayin da Wani Harsashi Ya Halaka Dalibar UNIZIK a Jihar Anambra Hoto: @Naija_PR
Asali: Twitter

A rahoton Sahara Repoerters, mummunan lamarin ya auku ne a mahaɗar Miracle da ke cikin birnin Awka ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba, 2023 da yammaci.

Yadda harsashin ya yi ajalin dalibar 100 Level a UNIZIK

Ganau kuma mazaunin Anguwar mai suna, Dickson Anayochi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ɗalibar da aka kashe tana karatu ne a tsangayar kimiyyar lafiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Anayochi ya kuma koka kan yanayin taɓarɓarewar tsaro a yankin yayin da ya yi kira ga rundunar 'yan sanda reshen jihar Anambra ta kafa shingen bincike a yankin.

"Dan Allah wannan saƙon ya isa kunnen Sufetan 'yan sanda na ƙasa, muna rokon a taimaka mana da shingen bincike a yankin Ifite da ke jami'ar UNIZIK saboda mun gaji da kai ƙorafi ga gwamnatin jiha."
"Yanzun abun ya zama kamar al'ada, har mun saba saboda yawan faruwarsa, abun da takaici."

Kara karanta wannan

"Abinda Ya Sa Iyaye Suka Daina Tura 'Ya'yansu Makarantu a Najeriya" Ministan Tinubu Ya Magantu

Yadda aka kashe ɗalibar jami'ar

Mutunen da lamarin ya faru a kan idonsu sun ce an kashe ɗalibar ne lokacin da wasu 'yan asiri ke ƙoƙarin bindige direban Keke-Napep, kamar yadda Punch ta rahoto.

Tsagerun sun rasa abin harinsu kuma ɗaya daga cikin harsasan da suka harba ne ya samu ɗalibar, wacce ke hanyar zuwa kasuwa.

Hatsarin Babbar Mota da Bas Ya Lakume Rayukan Mutum 5 a Anambra

A wani labarin na daban Wani mummunan hatsari ya yi ajalin fasinjojin motar bas mata 5 a jihar Anambra, wasu da dama sun ji raunuka.

Hadarin wanda ya auƙu da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Juma’a ya rutsa da mutane 10, maza uku da mata bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262