Tinubu Ya Dauko ‘Dan Takaran Shugaban Kasa, Ya Ba Shi Mukami a Gwamnatinsa

Tinubu Ya Dauko ‘Dan Takaran Shugaban Kasa, Ya Ba Shi Mukami a Gwamnatinsa

  • Tope Fasua ya zama mai bada shawara a kan tattalin arziki, zai taimakawa Gwamnatin Najeriya
  • Masanin tattalin zai yi aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a Aso Rock
  • Fasua ya sanar da haka a shafin X, ya na mai godewa wadanda su ka yi sanadiyyar ba shi mukamin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban kamfanin Global Analytics Consulting Limited, Tope Fasua ya samu mukami a gwamnati mai-ci a Najeriya.

Mista Tope Fasua ya yi magana a shafin X wanda aka fi sani da Twitter, ya ce ya zama mai bada shawara ga gwamnatin tarayya.

‘Dan kasuwa kuma ‘dan siyasar ya shaida haka ne a yammacin ranar Juma’ar nan a dandalin na X.

Tope Fasua
Tope Fasua zai ba Shugaban Kasa shawara Hoto: www.herald.ng
Asali: UGC

Tope Fasua zai yi aiki da Kashim Shettima

A jawabinsa, ya bayyana cewa zai yi aiki ne da Mai girma mataimakin shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima a ofishinsa a Aso Rock.

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamnan Jam'iyyar APC Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa? Gaskiya Ta Bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran ‘dan siyasar da ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ANRP zai rika ba gwamnati shawara a kan fanninsa.

Fasua zai taimaka wajen ganin yadda za a kawo cigaban tattalin arziki musamman ganin Kashim Shettima ne shugaban majalisar NEC.

A tsari da dokar kasa, wannan majalisa da ke da alhakin kula da tattalin arzikin kasa ta na karkashin ofishin mataimakin shugaban Najeriya.

"Saboda haka, an nada mutuminku a matsayin Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tattalin arziki a ofishin mataimakin shugaban kasa.
Sak abin da na ke so domin tasiri a kasa. Mu na godewa Ubangiji Madaukaki da wadanda su ka tunani da ni, su ka kuma jajirce a kai na."

- Tope Fasua

Fasua ya nuna cewa zai hidimtawa Ubangijinsa da kasarsa ne da wannan mukami da aka ba shi.

Kara karanta wannan

An Bar Najeriya Babu Kowa, Tinubu da Kashim Shettima Duk Sun Tafi Kasar Waje

Wanene Tope Fasua?

Fasua kwararren Akanta ne wanda ya yi zarra a jami’ar jihar Ondo a 1991, ya na da digiri na biyu a harkar kasuwanci daga wata jami’a a Landan.

Bayan kwas a Landan, Harvard da sauransu, ya yi aikin banki da Citizens Bank, Standard Trust Bank da Equatorial Trust Bank a gida da waje.

Mutanen Kudu maso yamma a gwamnatin Tinubu

Idan majalisar dattawa ta tantance Dr. Olayemi Micheal Cardoso, ku na da labari zai zama sabon Gwamnan CBN bayan dakatar da Godwin Emefiele.

Kamar ministan kudi, Akanta Janar, da sabon shugaban FIRS, Cardoso ya fito ne daga Kudu maso yamma, yankin da ke rike da mulkin Najeriya a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng