Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Gwamnan CBN da Mataimakansa 4
- Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa Dakta Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban banki CBN
- Shugaban ƙasar ya kuma naɗa mataimakan gwamnan guda huɗu duka na tsawon shekaru 5 idan majalisar dattawa ta tabbatar da su
- Ya ce yana sa ran mutanen da ya naɗa zasu yi aiki tukuri domin aiwatar da gyare-gyare a babban bankin Najeriya
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Dakta Olayemi Michael Cardoso, a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
NTA News ta wallafa a manhajar X cewa shugaba Tinubu ya naɗa sabon gwamnan CBN na tsawon shekaru 5 da zaran majalisar dattawa ta tabatar ta shi.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Jumu'a, 15 ga watan Satumba, 2023.
Tinubu ya naɗa mataimakan gwamnan CBN guda 4
Bugu da ƙari, shugaban ƙasa ya kuma amince da naɗa sabbin mataimakan gwamnan CBN guda 4 na tsawom shekaru 5 a matakin farko, da zaran majalisar dattawa ta amince da su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Waɗanda Tinubu a naɗa a matsayin mataimakan gwamnan sun haɗa da, Misis Emem Nnana Usoro, Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Mista Philip Ikeazor, da kuma Dokta Bala M. Bello.
Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa:
"Wannan naɗin ya yi daidai da sashe na 8 (1) na kundin dokokin babban banki CBN 2007, wanda ya baiwa shugaban ƙasa ƙarfin ikon nada gwamna da mataimakansa guda hudu (4) a CBN idan majalisar dattawa ta tabbatar."
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa ya na sa ran wadanda aka nada a sama za su yi aiki tukuru domin aiwatar da muhimman gyare-gyare a babban bankin Najeriya.
Wanda hakan zai kara kwarin gwiwa ga ‘yan Najeriya da abokan hulda na kasa da kasa domin bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da samun ci gaba mai dorewa da wadata ga kowa, in ji Tinubu.
Ganduje, Gwamnonin APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Jihar Imo
A wani rahoton kun ji cewa Dakta Ganduje, gwamnoni, ministoci da wasu ƙusoshin siyasa sun mamaye jihar Imo domin kaddamar da kwamitin kamfe.
Wannan na zuwa ne a shirye-shirye tunkarar zaben gwamnan jihar wanda zai gudana ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Asali: Legit.ng