Kamfanin NNPC Ya Samu Ribar Naira Biliyan 18.4 A Farkon Shekarar 2023
- Kamfanin mai na NNPC ya samu kazamin riba a farko wannan shekara da mu ke ciki na 2023 da kusan Naira biliyan 19
- Shugaban kamfanin, Mele Kyari shi ya bayyana haka a yau Juma'a 15 ga watan Satumba a Abuja
- Kyari ya bayyana haka ne a gaban kwamitin bincike na majalisar wakilai da kakakinta, Abbas Tajudden ke jagoranta
FCT, Abuja - Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ya ce sun samu ribar Naira biliyan 18.4 a farkon wannan shekara.
Kyari ya bayyana haka ne a yau Juma'a 15 ga watan Satumba a gaban kwamitin majalisar wakilai, Legit ta tattaro.
Meye NNPC ke cewa kan ribar da ya samu?
Ya ce akalla NNPC na da gidajen mai fiye da 900 a fadin kasar inda ya ke gudanar da kaso 30 na kasuwar man fetur.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mele Kyari na magana a gaban kwamitin da ke binciken mallakar makamishi na OVH inda kamfanin ya tabbatar da gaskiya, The Nation ta tattaro.
Ya ce:
"Shekaru biyar baya, NNPC ya samu mafi yawan riba ne a 2021 inda ya samu Naira biliyan 6.593.
"Amma a farkon wannan shekara mun samu ribar Naira biliyan 18.4 bayan mallakar OVH.
"Hakan ba wani abu ba ne kawai dai mun kara inganta harkokinmu ne da kuma fadada harkokin kasuwanci da hannun jari."
Legit Hausa ta ji ta bakin wasu kan ribar da kamfanin ya samu:
Mohammed Babangida ya ce idan so su ke su ce wannan ribar cire kudin tallafi ne sun yi kuskure.
Ya ce:
"Daman ai munsan su kam za su ci ribar cire tallafi amma mu fa babu komai sai wahalhalu."
Usman Faruk ya ce sun yi a banza ai kwanan nan sun sanar da tafka asara saboda satar mai a kasar.
Ya ce da ribar su da rashinsa duk daya tun da ba zai amfani talakawa ba musamman a Arewa.
Meye kakakin majalisa ya ce kan NNPC?
A martaninshi, kakakin majalisar wakilai, Honarabul Abbas Tajudden ya ce za su yi duk mai yiyuwa don taimakawa juna wurin gina kasar Najeriya.
Amma ya ce ba za su zama karnukan farautar hukumomin gwamnati ba, sai dai su hada kai don kawo ci gaba.
NNPC ya yi asarar $46bn kan satar mai
A wani labarin, kamfanin mai na NNPC ya bayyana cewa ya yi asarar Dala biliyan 46 saboda satar mai da ake yi a Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan 'yan Najeriya na cikin mawuyacin hali na tashin farashin kayayyaki bayan cire tallafin mai a kasar.
Yawan satar mai din ana samu ne a jihohin da ke da arzikin man fetur a kasar musamman a Kudancin Najeriya da suka hada da Bayelsa da Ribas da Akwa Ibom da sauransu.
Asali: Legit.ng