Shugaba Tinubu Na Shirin Kirkiro Sabuwar Ma'aikata? Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani
- Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin kawo karshen faɗace-faɗace tsakanin manoma da makiyaya a faɗin Najeriya
- Shugaban ƙasa ya ɗauki alƙawarin ne yayin gana wa da kwamitin garambawul ga kiwon dabbobi karƙashin Dakta Abdullahi Ganduje
- Kwamitin ya ba da shawarin kafa ma'aikatar dabbobi kuma shugaba Tinubu ya yi alƙawarin tattauna wa da gwamnonin jihohi
FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana shirinsa na kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a faɗin sassan ƙasar nan.
Tinubu ya kara da cewa gwamnatinsa za ta hada hannu da gwamnonin tare da neman mallakar filaye domin kiwo da bunƙasa harkokin kiwon dabbobi.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin ƙasa kan sake fasalin kiwon dabbobi karkashin jagorancin, Abdullahi Ganduje, wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar APC.
Tinubu ya gana da Ganduje da hafsoshin tsaro
Taron wanda ya gudana a fadar shugaban kasa ranar Alhamis ya samu halartar manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
The Cable ta rahoto cewa kwamitin bisa jagorancin Ganduje ya shawarci shugaban ƙasa ya kafa ma'aikatar dabbobi domin aiwatar da abubuwan da suka gano.
Da yake jawabi ga mambobin kwamitin, shugaba Tinubu ya ce:
"Zan yi magana da gwamnoni. Gwamnatin tarayya ta shirya sayen filaye domin kiwo da bunƙasa kiwon samar da dabbobi."
Tinubu ya zargi shugabanni
Shugaban ƙasa Tinubu ya ƙara da cewa rikicin makiyaya da manoma ya ci gaba da ruruwa a faɗin Najeriya saboda gazawar shugabanni da nuna halin ko in kula.
A cewar Tinubu, "Ba laifin manoma ko makiyaya bane, laifin duk ya rataya ne a kan shugabanni saboda sun gaza lalubo hanyar warware matsalar."
Wannan taron ya zo shekaru bayan majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC) ta amince da kafa kwamitin sauya fasalin kiwon dabbobi a 2019.
Matsalar Tsaro: Abinda Ya Sa Iyaye Ke Fargabar Tura 'Ya'yansu Makaranta, Ministan Tinubu
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa iyaye na tsoron tura 'ya'yansu makaranta ne saboda tsoron harin yan bindiga.
Ministan harkokin cikin gida, Tunji-Ojo ya ce yawan hare-haren da ake kaiwa makarantu tun 2014 babban abin damuwa ne.
Asali: Legit.ng