Tinubu Ya Nada Delu Yakubu A Matsayin Shugabar Hukumar NSIPA

Tinubu Ya Nada Delu Yakubu A Matsayin Shugabar Hukumar NSIPA

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Delu Bulus Yakubu a matsayin shugabar hukumar NSIPA bayan dawowarsa daga kasar Indiya
  • Tinubu ya bayyana nadin ne a yau Alhamis 14 ga watan Satumba a Abuja bayan dawowarsa daga kasar Indiya
  • Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta cire

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Delu Bulus Yakubu a matsayin shugabar Hukumar Jin Dadin Al'umma ta Kasa (NSIPA).

Wannan nadin nata zai tabbata ne idan majalisar Dattawa ta tantance ta tare da tabbatar da mukamin nata, Legit ta tattaro.

Tinubu ya nada Delu mukami
Tinubu Ya Nada Delu Yakubu Babban Mukami. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Waye ya sanar da nadin Delu da Tinubu ya yi?

Hadimin Tinubu a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a yau Alhamis 14 ga watan Satumba a Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci a Hukumar FIRS

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ngelale ya ce Yakubu ta na da kwarewa a bangaren jin dadin jama'a har na tsawon shekaru 15 inda ta yi digiri na biyu a kasar Ukraine.

Sanarwar ta ce:

"Tinubu na bukatar sabuwar shugabar hukumar ta nuna kwarewa da jajircewa da kuma gaskiya a hukumar.
"Ya bukaci hakan don ganin ta taimakawa gwamnatinsa wurin inganta rayuwar al'ummar kasar."

Tinubu ya nada Adelabu shugaban FIRS

A labari makamancin haka, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Zacch Adelabu Adelabu, a matsayin mukaddashin shugaban hukumar tara haraji ta kasa (FIRS).

Har zuwa nadinsa, Adelabu ya kasace mai ba shugaban kasar shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga.

An bukaci mukaddashin shugaban na FIRS da ya cike gibin hutun ritayar shugaban hukumar mai barin gado, Mohammed Nami.

Kara karanta wannan

Mai Dakin Tinubu Ta Yi Kyautar Ban Mamaki, Ta Rabawa Mutane N500m a Filato

Adelabu ya kasance tsohon kwamishinan kudi a gwamnatin tsohon gwamnan jihar Oyo, Marigayi Abiola Ajimobi.

Bola Tinubu ya yi sabbin nade-naden mukamai

A wani labarin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Aliyu Tijani Ahmed, a matsayin shugaban hukumar masu neman mafaka, baki da 'yan gudun hijira (NCFRMI).

Wannan na kunshe ne a wani rahoto da gidan talabin mallakin gwamnatin tarayya NTA News ya wallafa a shafin X, wadda aka fi sani da Twitter ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba, 2023.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya dawo daga kasar Indiya inda ya halarci taron shugabannin kasashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.