Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci a Hukumar FIRS

Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci a Hukumar FIRS

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sabon nadi mai muhimmanci a hukumar FIRS mai alhakin tara haraji a Najeriya
  • An nada Zacch Adelabu Adelabua matsayin mukaddashin shugaban hukumar FIRS
  • Har zuwa nadin nada, Adelabu ya kasance mai ba shugaban kasar shawara ta musamman kan harkokin kudaden haraji

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Zacch Adelabu Adelabu, a matsayin mukaddashin shugaban hukumar tara haraji ta kasa (FIRS), jaridar The Nation ta rahoto.

Har zuwa nadinsa, Adelabu ya kasace mai ba shugaban kasar shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga.

Tinubu ya nada Adelabu a matsayin mukaddashin shugaban FIRS
Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci a Hukumar FIRS Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Adelabu zai maye gurbin Mohammed Nami a matsayin mukaddashin shugaban FIRS

Adelabu ya kasance tsohon kwamishinan kudi a gwamnatin tsohon gwamnan jihar Oyo, Marigayi Abiola Ajimobi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Mai Neman Kujerar Gwamna Ya Zama Hadimi, An Cusa ‘Dan Takaran NNPP a Gwamnati

An bukaci mukaddashin shugaban na FIRS da ya cike gibin da hutun ritayar shugaban hukumar mai barin gado, Mohammed Nami wanda zai kammala wa’adinsa a karshen watan Disambar 2023 ya haifar.

A kwanan nan ne babban akawun wanda ya fito daga yankin Iwo-Ate a karamar hukumar Ogo-Oluwa ta jihar Oyo, ya samu shaidar digirin sa na digiri na uku a jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Najeriya, rahoton Vanguard.

Hukumar FIRS Ta Tara Tiriliyan 5.5 a Watanni 6, Harajin Da Ba a Taba Samu a Tarihi Ba

A gefe guda, mun ji a baya cewa hukumar FIRS mai alhakin tara haraji a Najeriya, ta shaida cewa daga Junairu zuwa karshen watan Yunin 2023, ta samu Naira tiriliyan 5.5. A tarihin Najeriya, Sun ta ce ba a taba yin lokacin da aka samu wadannan kudin shiga ba.

Shugaban FIRS na kasa, Muhammad Nami ya shaida haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a kan kudin da ake sa ran samu daga haraji a 2023-2024.

Kara karanta wannan

Shari’ar zabe, 50% da Hanyoyi 3 da Za a Iya Bi Wajen Gyara Zabe – Ministan Jonathan

Muhammad Nami ya yi magana a gaban majalisar tattalin arziki ta kasa watau NEC a taron da aka yi na ranar 20 ga watan Yulin 2023 a fadar Aso Rock.

Ba zan jira sai Tinubu ya gyara titi a Neja ba, Gwamna Bago

A wani labarin kuma gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana cewa daga yanzu jihar ba za ta sake jiran gwamnatin tarayya ta zo ta gyara hanyoyinta da suka lalace a fadin jihar ba, jaridar The Nation ta rahoto.

Ya bayyana cewa gwamnatin za ta nemi a biya ta abun da ta kashe idan aka kammala gyaran hanyoyin, yana mai cewa yanayin da hanyoyin tarayya ke ciki a jihar ba abu ne da za a iya bari ba a yanzu saboda rashin samun martani daga gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng