Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 4 Da Sace Wasu Da Dama a Jihar Sokoto

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 4 Da Sace Wasu Da Dama a Jihar Sokoto

  • Ƙauyen Giyawa na ƙaramar hukumar Goronyo ya fuskanci harin miyagun ƴan bindiga inda suka halaka bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba
  • Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a ƙauyen, sun halaka mutum huɗu tare da tasa ƙeyar wasu mutum 18 zuwa cikin daji
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa jami'anta sun bi bayan ƴan bindigan domin ceto mutanen da aja sace

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Sokoto - Ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Giyawa na ƙaramar hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto.

Jaridar Channels tv ta rahoto cewa ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum huɗu tare da sace wasu mutum 18.

Yan bindiga sun halaka mutum hudu a Sokoto
Yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Giyawa na jihar Sokoto Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Ƙaramar hukumar Goronyo na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ke yankin Gabashin jihar Sokoto, inda ake fama da matsalar rashin tsaro da hare-haren ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Jajantawa Libya Yayinda Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sanadin Ambaliyar Ruwa Ya Kai 6,000

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar harin

Mataimakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Ahmed Rufai, ya bayyana cewa tun da farko mutum 18 ne ƴan bindigan da suka sace, sannan sun haɗa da dabbobi sun yi awon gaba da su, rahoton Nigerian Tribune ya tabbatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, ya bayyana cewa mutum bakwai daga cikin waɗanɗa aka sacen, sun gudu daga hannun ƴan bindigan inda suka dawo ƙauyen wanda mutane da dama sun yi masa ƙaura domin tsira da rayuwarsu.

Duk da cewa wasu majiyoyi a ƙauyen da lamarin ya auku sun yi iƙirarin cewa sama da mutum 30 ƴan bindigan suka sace, ƴan sanda sun nanata cewa mutum 11 kawai suka rage a hannun ƴan bindigan.

Rundunar ƴan sandan ta kuma bayyana cewa jami'anta sun bi bayan ƴan bindigan sannan suna ƙoƙarin ganin zaman lafiya ya dawo a ƙauyen da yankunan da ke kusa da shi.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Mambobin Kungiyar NURTW Suka Ba Hammata Iska a Abuja, Bayanai Sun Fito

Yan Bindiga Sun Mamaye Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnna jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya koka kan yadda yawaitar ayyukan ƴan bindiga ke ƙaruwa a jihar, inda ya ce lamarin ya sha kansu.

Ya bayyana cewa yaƙin da jami'an tsaro ke yi da ƴan bindiga a wasu jihohin ya sanya suna yin hijira zuwa jiharsa domin samun maɓoya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng