Yadda Dakarun Sojoji Suka Kama Makashin Dorathy Jonathan a Kudancin Kaduna
- Sojojin Najeriya sun kama Lot Dauda kan kisan wata matashiya, Dorathy Jonathan a kudancin Kaduna
- Dauda wanda dakarun Operations Safe Haven suka kama shi ya tona cewa ya aikata laifin ne tare da wani mutum
- A cewar shi, ya kashe Dorathy ne lokacin da ya nemi kwanciya da ita amma ta fafata da shi a wata gona
Jihar Kaduna - Dakarun Operations Safe Haven sun kama wani matashi mai suna Lot Dauda, wanda ya kashe Dorathy Jonathan a kudancin jihar Kaduna.
An kashe matashiyar yayin da ta je debo itatuwa a kauyen Afana da ke karamar hukumar Zango Kataf a jihar a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba.
Rundunar sojin Najeriya ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, kamun Dauda da aka yi ya biyo bayan alwashin da kwamandan Operation SAFE HAVEN, Manjo Janar AE Abubakar ya sha na gurfanar duk masu aikata laifi a gaban doka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rundunar sojin ta yi bayanin cewa an kama Dauda ne ta farautarsa da dakarun sojoji suka fara yi bayan samun bayanan sirri.
Wanda ake zargin ya ce shi ya kashe Dorathy Jonathan
Wanda ake zargin ya tona cewa ya aikata laifin tare da wani mutum wanda ya tsere a yanzu.
"Makashin ya bayyana cewa ya tunkari Misis Dorathy yayin da take aiki a wata gona sannan ya so kwantawa da ita ta karfin tuwo inda ita kuma ta fafata da shi wanda ya kai ga ya yi mata kisan gilla."
Rundunar sojin ta bayyana cewa za a gurfanar da Dauda a kotu da zaran an kammala bincike.
“‘Yan Bindiga Sun Mamaye Mu”, Gwamnan Bauchi Ya Koka
A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya koka kan ayyukan 'yan bindiga a jihar inda ya ce sun fara shan kansu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa yayin da ya karbi bakuncin sarakunan jihar Bauchi wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati a ranar Asabar, 14 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng