Sanatan Abuja Ta Caccaki Wike Kan Nadin Sakatarori 8 Na Hukumar FCTA

Sanatan Abuja Ta Caccaki Wike Kan Nadin Sakatarori 8 Na Hukumar FCTA

  • Sanata Ireti Kingibe ta babban birnin tarayya Abuja, ta gargadi ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da ya daina bayyana kansa a matsayin gwamnan FCT
  • Kingibe ta yi nuni da cewa yakamata a ce majalisa ta tantance sakatarori takwas na hukumar FCT da aka naɗa kwanan nan
  • Da take jawabi ga jama'ar mazabarta a wani taron manema labarai, Kingibe ta ce an zaɓen ta aka yi amma Wike naɗa shi aka yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Ireti Kingibe, sanatan da ke wakiltar birnin tarayya Abuja, ta gargaɗi ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike kan wuce gona da iri ba tare da tuntuɓar majalisar tarayya ba.

A cewar rahoton ThisDay, Kingibe ta bayyana cewa majalisar tarayya ita ce za ta gudanar da ayyukan majalisa na hukumar babban birnin tarayya (FCTA) kamar yadda majalisar dokoki ta jiha ke yi wa gwamnatin jiha.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Ministar Tinubu da Kitsa Yadda Za a Tsige Shugaban Majalisar Tarayya

Kingibe ta caccaki Nyesom Wike
Sanata Kingibe ta gargadi Wike kan wuce gona da iri Hoto: Nyesom Wike, Ireti Kingibe
Asali: Twitter

Kingibe ta caccaki nadin muƙamai 8 da Wike ya yi

Sanatan ta yi wannan tsokacin ne a lokacin da ta ke nuna rashin dacewar rantsar da wasu sakatarorin FCTA guda takwas da ministan ya yi kwanakin baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta bayyana cewa Wike ba shi da hurumin nadawa da kuma ƙaddamar da sakatarorin, kuma wasu daga cikinsu ’ƴan asalin babban birnin tarayya ne.

Ta ce kamar yadda majalisar dokoki ta jiha take ga gwamnatocin jihohi, haka ma FCTA take ga majalisar tarayya.

Yayin da take jawabi a mazabarta, Sanatan ta bayyana cewa:

"Minista ba ya da ikon zartarwa, yana aiki ne kafaɗa da kafaɗa da majalisar tarayya da kuma shugaban kasa wajen gudanar da ayyukan babban birnin tarayya Abuja."

"Ni ce wakiliyar ku ba Wike ba": Ireti ga ƴan mazaɓarta

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

Sanatan ta tunatar da al'ummar mazabarta cewa ita ce wakiliyarsu ba Wike ba, domin ita an zaɓen ta aka yi amma Wike Shugaban ƙasa Tinubu ne ya naɗa shi.

Sai dai ta nuna ƙwarin gwiwar ta kan yin aiki tare da tsohon gwamnan na jihar Rivers.

A kalamanta:

"Dole ne ku tuna cewa ni da minista muna da mabambantan ayyuka. Jama'a ne suka zabe ni, alhakin ku na kai na, mutanen FCT, ba shi ba. Amma idan muka yi aiki tare, ina fatan za mu iya hada kan muradun mu."

Majalisa Ta Musanta Karbar Tallafin N100m

A wani labarin kuma, majalisar wakilai ta fito fili ta musanta zargin cewa mambobinta sun samu tallfin N100m daga asusun gwamnatin tarayya.

Majalisar ta bayyana cewa zargin wanda ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta yi, ba ya da tushe ballantana makama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng