Daga Villa Zuwa Gonar Daura: Shehu Ya Bayyana Sabon Aikin Buhari Kwana 100 Bayan Barin Ofis
- Kimanin kwana 100 kenan tunda Muhammadu Buhari ya bar ofis a matsayin shugaban kasar Najeriya na 15 sannan ya koma mahaifarsa ta Daura, jihar Katsina
- Garba Shehu, hadiminsa, ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da tsohon shugaban kasar yake yi, da kuma nasarorin da ya samu yayin da yake ofis
- Shehu ya ce koda dai babu wani shugaba da ba shi da kura-kurai, babu wanda zai yi tantama a kan kyawawan manufar Buhari ga kasa
FCT, Abuja - Garba Shehu, kakakin tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ubangidansa na gonarsa a yanzu haka.
Shehu ya ce gonar bata samu cikakken kulawar da take bukata ba a lokacin da Buhari baya nan.
"Tarihi zai yiwa Buhari adalci": Shehu
Kakakin tsohon shugaban kasar ya ce Buhari yana zuwa gonarsa sau hudu a mako kuma "ya ji dadin yadda amfanin gona da dabbobin sa suke a yanzu".
Jerin Abubuwa 2 Daga Cikin Tsare-tsaren Buhari Da Tinubu Ya Yi Watsi Da Su Watanni 4 Da Hawa Karagar Mulki
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shehu ya rubuta a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba:
"A wannan makon, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika kwana 100 da barin ofis bayan kammala wa'a din mulki na shekaru hudu sau biyu a matsayin shugaban kasar Najeriya.
"Yayin da wasu a kasar suka ji dadin cewa ba ya kan mulki, akwai wasu ma da suka ci gaba da mutunta shi da kuma sonsa.
"A shekaru takwas da ya shugabanci kasar, Muhammadu Buhari ya dauki matakai da dama kuma a matsayinsa na dan adam, mai yiwuwa akwai daya zuwa biyu da za su zama ba daidai ba. Amma babu wani mutum, hatta masu adawa da za su iya nuna shakku kan manufofinsa a lokacin da aka dauki wadannan matakan.
"Muhammadu ya yi iya nasa kokarin sannan ya tafi. Tarihi zai yi masa hukunci, kuma na adalci a tunanina."
Kira 1 Atiku Zai Yi Wa Bola Tinubu Ya Kori Wike A Mukaminsa Na Minista
A wani labarin kuma, mun ji cewa jigon jam'iyyar PDP, Daniel Bwala ya ce kiran waya daya daga Atiku ya isa a kori Nyesom Wike a mukaminsa.
Bwala ya bayyana haka ne yayin hira da Arise TV a ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, kamar yadda Legit ta tattaro.
Asali: Legit.ng