Jami'an 'Yan Sanda Sun Cafke Korarren Jami'ansu Kan Zargin Sata Da Damfara
- Rundunar 'yan sanda a jihar Ogun sun cafke wani matashi da zargin bayyana kansa a matsayin jami'in dan sanda
- Wanda ake zargin Anas Yusuf ya shiga aikin dan sanda tun a shekarar 2016 inda ya yi aiki a jihohin Sokoto da Legas kafin a koreshi a aiki
- Kakakin rundunar 'yan sanda a yankin na 7, Akeem Adeoye ya bayyana haka ne a ranar Laraba 13 ga watan Satumba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ondo - Jami'an tsaro sun cafke korarren dan sanda kan zargin sata da kuma damfara a jihar Ondo.
Wanda ake zargin, Yusuf Anas an kama shi ne bayan ya sayi waya da kirkirar sakon tura kudi na bogi a jihar.
Meye tsohon dan sanda ya sata?
An dauki Anas aikin dan sanda a shekarar 2016 inda ya yi aiki a jihar Sokoto da kuma Legas, Daily Trust ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani aka kore shi a aikin bayan ya gudu daga aikin nasa tare da kin bin dokokin hukumar.
Kakakin rundunar 'yan sanda a yankin na 7, Akeem Adeoye ya bayyana haka ne a ranar Laraba 13 ga watan Satumba.
Adeoye ya ce an kama wanda ake zargin ya na bayyana kansa a matsayin jami'in dan sanda duk da korarshi da aka yi a aikin, cewar Vanguard.
Yadda aka kama tsohon dan sanda da sata
Ya ce:
"A ranar 8 ga watan Mayu, Anas ya ci gaba da nuna kansa a matsayin jami'in dan sanda inda ya je siyan waya ta Naira dubu 102 a shago.
"Bayan ya karbi wayar kirar Tecno Spark 10 sai ya kirkiri sakon tura kudi na bogi."
Adeoye ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan korafi zuwa ofishin mataimakin sifetan 'yan sanda a yankin.
Ya kara da cewa an kama Anas ne bayan samun bayanan sirri da kuma bincike da aka gudanar.
Direban Mota Ya Murkushe Jami'in FRSC Har Lahira A Abuja
A wani labarin, wani direban babbar mota ya yi ajalin jami'in Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a kan titin Abuja zuwa Kaduna.
Marigayin mai suna Idris Hamisu ya rasu ne a yau Talata 12 ga watan Satumba a kokarin bin umarnin shugabanninsa na kai motar zuwa ofishinsu.
Asali: Legit.ng