Fasto Ayodele Ya Ce Farashin Siminti Ba Zai Dawo Kasa Ba Har Zuwa N2,000
- Shaharareen Fasto, Elijah Ayodele ya fadawa ‘yan Najeriya cewa su manta da maganar dawo da farashin siminti kasa a nan gaba
- Faston ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Laraba 13 ga watan Satumba inda ya ce hakan na da matukar wahala
- Shugaban kamfanin siminti na BUA, Abdussamad Rabiu ya ce farashin siminti zai fado kasa da zarar ya kammala kamfanonisa biyu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Legas - Shahararren Fasto kuma shugaban Evangelical Spiritual Church, Elijah Ayodele ya yi martani kan farashin siminti a Najeriya.
Faston ya bayyana cewa zai yi wahala farashin siminti ya dawo kasa kamar yadda ake zato, Legit ta tattaro.
Meye malamin ke cewa kan farashin siminti?
Ya ce abu ne mai wahala ace farashin simintin ya sauko har Naira dubu biyu kamar yadda ya ke a baya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce:
“Kamfanin siminti na Dangote da BUA ba za su sauko da farashi ba zuwa Naira dubu biyu.”
Fasto ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 13 ga watan Satumba.
Ya ce ‘yan Najeriya kawai abin da za su yi shi ne addu’ar samun ingantaccen tattalin arziki a kasar.
Ya kara da cewa:
“Idan mu na magana a kan siminti, ban ga hanyar da za a dawo da farashin siminti zuwa Naira dubu biyu ko dubu daya da dari biyar ba.
“Ku manta da hakan, farashin zai ci gaba da tashi ne sama, Dangote da BUA ba su da ikon dawo da shi kasa zuwa N2,000 ko N1,500, ko gwamnati ma ba ta da wannan ikon.”
Meye kamfanin BUA, Dangote ke cewa kan simintin?
Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Matashi Ya Farmaki Malamin Addinini Tare Da Ajalinsa Da Adda, An Bazama Nemanshi
A baya an zargi kamfanin Dangote da cewa ya na siyar da siminti da tsada a Najeriya fiye da sauran kasashen Afirka.
Amma kamfanin ya karyata wannan jita-jita inda ya ce simintin ya fi araha a Najeriya fiye da sauran kasashen da ake magana a kansu.
Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu ya bayyana cewa za a samu faduwar farashin siminti da zarar ya kammala sabbin kamfanoninsa biyu zuwa karshen wannan shekara.
Kamfanin BUA Ya Shirya Rage Farashin Siminti A Najeriya
A wani labarin, Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu ya ce sun shirya tsaf don rage farashin siminti a fadin kasar.
Kamfanin ya ce zai yi hakan ne don dafa wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu wurin inganta tsare-tsarensa na tattalin arziki.
Asali: Legit.ng