Hadimin Atiku Ya Yi Wa Shugaba Wankin Babban Bargo

Hadimin Atiku Ya Yi Wa Shugaba Wankin Babban Bargo

  • Daniel Bwala, jigo a jam'iyyar PDP kuma tsohon hadimin Atiku Abubakar ya zargi Shugaba Tinubu da yin mulkin ƙasar nan cikin waƙa
  • Bwala ya bayyana kwanaki 100 kan mulki na Tinubu a matsayin waɗanda ƴan Najeriya ba su ji daɗinsu ba
  • Babban lauyan ya bayyana cewa dole ne shugaban ƙasar ya mayar da hankali wajen mulki a maimakon tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje domin ɗaukar hoto

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Daniel Bwala, tsohon hadimin Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, ya shawarci Shugaba Tinubu ya mayar da hankali kan mulki a maimakon tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje domin ɗaukar hoto.

Da yake magana a gidan talbijin na AriseTv a yammacin ranar Talata, 12 ga watan Satumba, babban lauyan ya yi bayanin cewa kwanaki 100 na Tinubu ba su haifar da ɗa mai ido ba, sannan yana buƙatar ya mayar da hankali wajen gina ƙasa maimakon yawon ɗaukar hoto a ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Neman Dawowa Ɗanye, Tsagin Atiku Ya Maida Martani Mai Zafi Ga Wike

Daniel Bwala ya caccaki Shugaba Tinubu
Bwala bai yaba da kamun ludayin mulkin Tinubu ba Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Shugaba Tinubu yana mulki cikin waƙa

Jigon na jam'iyyar PDP ya kuma yi zargin cewa yarjeniyar da Tinubu ya cimmawa da wasu shugabannin ƙasashen duniya, ciki har da wacce ya cimmawa a ƙasar haɗaɗɗiyar daular Larabawa (UAE), ba gaskiya ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Da zai zama labari mai daɗi idan alal misali, gaskiya ne. Abin takaici, ba haka ba ne. Ana cewa ana yin yaƙin neman zaɓe ne da waƙa, amma ana yin mulki a kan karagar mulki, amma ga dukkan alamu har yanzu a waka suke yi.”

"Kwanaki 100 na Tinubu ba su haifar da ɗa mai ido ba", hadimin Atiku

A na shi ra'ayin, Bwala ya bayyana cewa abin da ya kamata a yi la'akari da shi a matsayin nasara duk ƴan Najeriya ne za su gani ba ƙirƙirar tunanin wani ba. A tambayi ƴan Najeriya ko sun sami wani gagarumin sauyi, za su ce ko kaɗan.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Bayyana Abin Da Atiku, Peter Obi Za Su Tarar a Kotun Koli

A cewar Bwala, ɓangarorin ilmi, lafiya, ƙwadago an cigaba da fuskantar ƙalubale waɗanda har yanzu an kasa magance su.

Sanatan PDP Ya Yi Nasara a Kotu

A wani labarin kuma, sanatan jam'iyyar PDP na Enugu ta Yamma, Injiniya Osita Ngwu, ya yi nasara a kotun zaɓen kan ƙarar da abokan takararsa suka shigar a kotun zaɓe.

Kotun zaɓen ta yi fatati da ƙararrakin da ƴan takarar jam'iyyun APC da Labour Party suka shigar suna ƙalubalantar nasarar da ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng