Dakarun Soji Sun Kutsa Cikin Dajin Sambisa, Sun Sheke Yan Ta'adda a Borno

Dakarun Soji Sun Kutsa Cikin Dajin Sambisa, Sun Sheke Yan Ta'adda a Borno

  • Jami'an rundunar sojin Operation Haɗin Kai sun halaka 'yan ta'adda da dama a wani samame da suka kai dajin Sambisa
  • Kakakin hukumar sojin sama ya bayyama cewa sojojin sun yi wa yan ta'addan ruwan wuta ta sama bayan samun bayanan sirri
  • A cewarsa, bayan harin sun gano cewa samamen ya sheƙe su da yawa kana ya tarwatsa sansaninsu a Suwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Borno - Dakarun sojin saman Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai da ke Arewa maso Gabas sun tarwatsa ragowar 'yan ta'addan da suka hana zaman lafiya a yankin dajin Sambisa na jihar Borno.

Gwarazan sojojin sun samu wannan gagarumin nasara ne biyo bayan luguden bama-baman da suka yi kan mafakar 'yan ta'addan a garin Suwa, ƙaramar hukumar Kala Balge.

Sojin Najeriya sun samu nasara a Borno.
Dakarun Soji Sun Kutsa Cikin Dajin Sambisa, Sun Sheke Yan Ta'adda a Borno Hoto: Army
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa samamen, wanda jiragen sojin saman suka kai da sanyin safiyar ranar Litinin, ya halaka tulin mayaƙan ƙungiyar 'yan ta'adda a dajin.

Kara karanta wannan

Tallafi: Yayin Da Ake Halin Kunci, Matasa Sun Yi Warwason Shinkafa Kan Motoci 3 A Arewa, Bayanai Sun Fito

Yadda sojoji suka tarwatsa 'yan ta'adda a Sambisa

Kakakin hukumar sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet, ya shaida wa 'yan jarida a Abuja ranar Talata cewa an kai wannan farmaki ne bayan tattara bayanan sirri.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce bayanan sirrin da sojojin suka samu ya nuna cewa 'yan ta'addan na ƙulle-kulle kai sabon mummunan harin kan mutane.

Ya ce bayanan da aka samu sun kuma nuna cewa kungiyar ta ‘yan ta’addan ta kammala shirin kai hari kan sansanin sojoji da ke Rann a karamar hukumar Kalabalge ta jihar Borno.

A cewarsa, nan take aka tura sojoji suka kai hari ta sama kuma bayan gudanar da bincike an gano cewa ruwan wutan ya halaka yan ta'adda da dama tare da lalata maɓoyarsu.

Haka zalika, wannan nasara ta gurgunta ƙarfin 'yan ta'addan ta yadda ba zasu iya kai hari kan jami'an tsaro ko fararen hula ba, kamar yadda The Cable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ba Daɗi: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Mummunan Hari, Sun Halaka Jami'an Tsaro a Jihar Arewa

“A kokarin kakkabe ragowar ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas da tsaftace shiyyar daga ayyukan ta'addanci, dakarun sojin saman Operation Hadin Kai sun kai hari Suwa karamar hukumar Kala Balge a Borno ranar 11 ga Satumba."
"Idan dai za a iya tunawa, garin Suwa ya kasance tungar ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Gezuwa kusa da dajin Sambisa har sai da sojoji da sauran jami’an tsaro suka fatattake su."

- Edward Gabkwet.

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Sace Fasinjojin Motocin Gwamnatin Jihar Benue

A wani rahoton na daban Wasu 'yan bindiga sun tare motocin gwamnatin jihar Benuwai, sun yi awon gaba da fasinjoji aƙalla 10.

Matafiyan sun faɗa hannun miyagun ' yan bindigan ne a yankin Okene da ke jihar Kogi bayan sun baro Makurdi, babban birnin jihar Benuwai sun nufi jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262