Jerin Tsare-tsaren Buhari 2 Da Tinubu Ya Yi Fatali Da Su Bayan Hawa Karagar Mulki
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rusa tsare-tsaren tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari guda biyu watanni hudu kacal a kan mulki.
A lokacin kamfe na zaben 2023, Tinubu ya yi alkawarin ci gaba daga inda Buhari ya tsaya don kawo ci gaba a Najeriya.
Da alamu shugaban ya saba wannan alkawari ganin yadda ya rusa tsare-tsaren Buhari har guda biyu, Legit ta tattaro.
Bayan watanni hudu kacal a kan mulki, Tinubu ya yi watsi da tsare-tsaren Buhari tare da cewa ba su da amfani.
Abin mamaki shi ne daya daga cikin tsare-tsaren ya shafi tattalin arziki yayin da daya ya shafi tsaro da kuma kabilanci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsare-tsaren guda biyun sun hada da:
1. Biyan bashi da kusan kaso 90 na kudin shiga
Tinubu ya sha alwashin dakatar da biyan kusan kaso 90 na bashin kasar da kudaden shiga da ake samu.
Ya bayyana tsarin da cewa zai durkusar da Najeriya kuma ba ya goyon bayan haka ko kadan.
Lokacin da Buhari ke kan mulki, majalisar tattalin arziki ta ba da shawarar biyan basuka kusan kaso 90 da kudaden shiga na kasa.
Tinubu ya ce:
"Ba zai yiyu mu ci gaba da biyan kusan kaso 90 na basuka da kudaden shiga ba, wannan hanya ce ta kashe kasa.
"Dole mu nemo hanyoyi ko da za mu sha wahala don mu farka daga bacci kuma mu samu daraja a idon duniya."
2. Kiwon shanu tare da yin ruga
Bola Tinubu ya yi fatali da ayyukan makiyaya a Najeriya yayin da yake jawabi ga 'yan Najeriya a indiya.
Ya ce kiwon shanu a Najeriya abin kunya ne ganin yadda ya mai da likitocin dabbobi marasa amfani a kasar, Premium Times ta tattaro.
Idan ba a mantaba, tsohon shugaban kasa, Buhari ya samar da hanyoyin kiwo ga makiyaya don dakile rikicinsu da manoma.
Tinubu ya fadi yadda zai kawo karshen ciwo bashi
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya yi alkawarin kawo karshen kashe kudi wurin biyan bashi da kasar ke yi duba da kankanin kudin shiga da gwamnati ke da shi.
Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne yayin kaddamar da kwamitin shugaban kasa na nazarin kudi da sauye-sauyen dokokin haraji.
Asali: Legit.ng