Fashola Ya Bayyana Mukaminsa a Gwamnatin Shugaba Tinubu

Fashola Ya Bayyana Mukaminsa a Gwamnatin Shugaba Tinubu

  • Babatunde Fashola, tsohon ministan gidaje da ayyuka ya bayyana cewa yana da muƙami mai muhimmanci a gwamnatin Tinubu
  • A cewar tsohon gwamnan na Legas, sabon aikinsa a gwamnatin nan shi ne taka rawarsa a matsayin ɗan ƙasa
  • Fashola ya yi nuni da cewa Najeriya tana da sama da mutum 200m sannan ba kowa ba ne zai zama minista ko ƙusa a gwammnati

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ojo, jihar Legas - Babatunde Fashola, tsohon ministan ayyuka da gidaje, ya bayyana cewa yana da muƙami mai muhimmanci a gwamnatin Shugaba Tinubu.

A cewar tsohon gwamnan, gwamnatin Tinubu tana ƙyanƙyashe sabbin shugabanni, sannan ba ya bukatar muƙami kafin ya taka rawarsa a matsayinsa na ɗan Najeriya.

Fashola ya bayyana mukaminsa a gwamnatin Tinubu
Fashola ya bayyana sabon mukaminsa a gwamnatin Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Babatunde Fashola
Asali: Twitter

Fashola ya yi magana yiwuwar samun muƙami a gwamnatin Tinubu

A cewar rahoton PM News, ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin ƴan jarida a jami'ar jihar Legas a Ojo ranar Talata, 12 ga watan Satumban 2023.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Ce Najeriya Na Buƙatar Naira Tiriliyan 21 Domin Magance Wata Gagarumar Matsala

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yi magana ne dai a kan rawar da zai taka a wannan gwamnatin da kuma yiwuwar ya samu muƙami.

Fashola ya faɗi dalilin da ya sanya dole ƴan ƙasa su taka rawa a gwamnatin Tinubu

Ya yi nuni da cewa Shugaba Tinubu minista ɗaya kawai yake buƙata daga kowacce jiha, wanda kuma ya yi hakan. Saboda haka zai taka rawarsa a matsayinsa na ɗan ƙasa.

Tsohon gwamnan ya yi nuni da cewa babu isassun hukumomin gwamnati da ƴan Najeriya sama da miliyan 200 za su samu muƙami a ciki, inda ya ƙara da cewa ba kowa ba ne zai samu muƙami a gwamnati amma dole ne kowa ya taka rawarsa a matsayin ɗan ƙasa.

Wani ɓangare na kalamansa na cewa:

"Dole ne dukkanmu mu taka rawa a matsayinmu na ƴan kasa, sannan ɗan ƙasa baya bukatar muƙami don yin hidima."

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Bayyana Yankunan Da Za Su Ci Gajiyar Mulkin Shugaba Tinubu

Akeredoƙu Ya Sallami Hadiman Mataimakinsa

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akinkunrin Akeredolu, ya sallami dukkanin hadiman mataikinsa.

Korar dai na zuwa ne bayan Akeredolu ya cigabba da mulkar jihar bayan ya dawo daga jinyar wata uku da ya yi a ƙasar Jamus. Ana ganin dangantaka ta fara tsami a tsakanin gwamnan da mataimakinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng