Kungiyar MURIC Ta Caccaki Fastoci Kan Barazana Ga Alkalan Kotun Koli

Kungiyar MURIC Ta Caccaki Fastoci Kan Barazana Ga Alkalan Kotun Koli

  • Kungiyar MURIC ta yi Allah wadai da matakin da gamayyar Fastoci su ka yi na yi wa alkalan kotun koli barazana
  • Kungiyar ta ce madadin Fastocin su ja kunnen magoya bayansu kan zage-zage da su ke, sun biye musu da barazana
  • Ta bukaci alkalan kotun koli da kada su tsorata da barazanar Fastocin inda su ka hore su da dogewa kan adalci a kotun

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta soki gamayyar Fastocin Najeriya kan yi wa kotun koli barazana.

MURIC ta yi gargadin ne bayan Fastocin sun yi wa kotun koli barazana kan shari'ar da za a yi na zaben shugaban kasa, Legit ta tattaro.

MURIC ta soki gamayyar Fastoci kan alkalan kotun koli
Kungiyar MURIC Ta Yi Martani Kan Gamayyar Fastoci. Hoto: Ishaq Akintola.
Asali: UGC

Meye ya jawo gargadin na MURIC?

Idan ba a mantaba, kotun sauraran kararrakin zaben ta tabbatar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a ranar Laraba 6 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Jerin Ministocin Tinubu Da Kotun Zabe Ta Ayyana a Matsayin Wadanda Suka Lashe Zaben Yan Majalisun Tarayya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotun ta kori karar Atiku Abubakar da Peter Obi saboda karancin hujjoji.

Yayin da 'yan takarar jam'iyyun adawa su ka sha alwashin daukaka kara zuwa kotun koli.

Shugaban gamayyar Fastocin, Lucius Iwejuru ya bukaci kotun kolin ta yi adalci yayin da 'yan takarar ke tunkararta da korafi.

Martanin MURIC kan gamayyar Fastocin

Da ta ke martani, MURIC ta bakin daraktanta, Farfesa Ishaq Akintola ya soki Fastocin da kin goyon bayan hukuncin kotun.

Akintola kamar yadda Daily Trust ta tattaro, ya ce:

"Mun fahimci son kai daga bangaren Fastocin zuwa ga 'yan takarar adawa.
"Wannan barazana da kuma cin mutunci na alkalan kotun da Fastocin su ka yi ba za mu amince da shi ba."

Akintola ya kuma caccaki Fastocin wurin gagara kwaban magoya bayan 'yan adawa kan cin mutunci da su ke yi da zage-zage.

Kara karanta wannan

An kuma: Sanatan APC ya yi nasara kan PDP a gaban kotu, an yi watsi da duk wani zargi

Ya bukaci kotun da kada ta bari wannan barazana daga Fastocin ya hana su yin adalci.

MURIC ta soki gwamnan Legas kan tauye hakkin Musulmai

A wani labarin, Hukumar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta ja hankalin gwamnatin jihar Lagos kan yadda aka tsara jadawalin jarabawar zango na uku a jihar.

Daliban makarantun gwamnati sun fara jarrabawar zango na uku a ranar Alhamis 13 ga watan Yuli.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin jihar ta yi mai yiyuwa don kare hakkin addinin Musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel