Najeriya Ta Rasa Mataki Na 1 A Jerin Kasashe Da Su Ka Fi Samar Da Mai A Nahiyar Afirka
- Najeriya na samun matsaloli ta bangarori da dama musamman a harkokin samar da danyen mai a duniya
- Wannan na zuwa ne bayan kasar ta rasa matakin farko na kasashen Nahiyar Afirka da su ka fi samar da man
- A yanzu, Libya ta karbe matakin farko yayin da Angola ta kasance na biyu a jerin kasashe mafi samar da mai
FCT, Abuja - Najeriya na daga cikin kasashen da ke ba da gudunmawa wurin samar da mai a duniya duba da tarun arzikin kasar na mai.
Nahiyar Afirka na ba da gudunmawar fiye da kaso 8 na mai a duniya, amma farkon 2023, an samu matsaloli da dama, Legit ta tattaro.
Meye rahoton ya ce kan Najeriya a samar da mai?
Rahoton Energy Chamber ya ce daga watan Janairu zuwa Mayu Nahiyar ta yi asarar fiye da gangan mai dubu 180 a ko wace rana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Najeriya ta rasa matakin farko a Nahiyar wacce ta fi kowa kasa samar da mai bayan samun matsalolo masu tarin yawa da su ka hada da satar mai din musamman a jihohin Kudu maso Kudu.
Kasar ta fado har mataki na uku bayan Libya da Angola sun karbe matakin farko da na biyu a Nahiyar a matsayin mafi samar da man.
Najeriya ta yi asarar fiye da gangan mai dubu 165 a rana cikin watanni biyar na farkon shekarar 2023.
Wasu kasashe ne gaba da Najeriya kan samar da mai?
Legit ta jero muku kasashen da su ka fi samar da mai a Nahiyar Afirka:
1. Libya
2. Angola
3. Najeriya
4. Algeriya
5. Masar
6. Congo
7. Gabon
8. Sudan
9. Ghana
10. Chad
Najeriya Ta Yi Asarar $46bn Na Danyen Mai Saboda Sata
A wani labarin, Kamfanin mai na NNPC ya ce ya yi asarar fiye da Dala biliyan 46 na gangan danyen mai miliyan 612 a cikin shekaru 10.
NNPC ya ce yawan satar mai da ake a kasar ya wuce hankali wanda hakan ke jawo wa kamfanin da Najeriya asara ta makudan kudade.
Hukumar Hakar Ma'adinai ta Najeriya (NEITI) ita ta tabbatar da haka a wani rahoto da ta fitar yayin wata ganawa ta musamman.
Asali: Legit.ng