Shugaba Tinubu Ya Bada Umarnin Bincike Kan Yawaitar Hatsarin Jirgin Ruwa a Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Bada Umarnin Bincike Kan Yawaitar Hatsarin Jirgin Ruwa a Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar da ke kula da tsaron ruwa ta gudanar da bincike kan haɗurran jiragen ruwan da suka faru kwanan nan
  • Shugaban kasan ya kuma jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon ibtila'in tare da tabbatar da kare irin haka nan gaba
  • Ya buƙaci hukumomin gwamnati su sake nazari kan dokokin ayyukan jiragen ruwa kuma su tabbatar da ana bin kowace doka

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan hadurran jiragen ruwa da ke yawan faruwa a Najeriya.

Tinubu ya ba da wannan umarni ne ga hukumomin tsaron teku biyo bayan hadurran Kwale-kwale guda biyu da aka yi a jihohin Adamawa da Neja, wanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Kara karanta wannan

Hatsarin Kwale-Kwale a Neja: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 30, NSEMA

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Bada Umarnin Bincike Kan Yawaitar Hatsarin Jirgin Ruwa a Najeriya Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta tattaro cewa akalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu bayan wani jirgin ruwa ya kife a Gbajibo da ke ƙaramar hukumar Mokwa a jihar Neja ranar Lahadi.

Kafin haka, mutane takwas ne suka mutu yayin da wasu bakwai kuma suka ɓace a wani hatsarin kwale-kwale a tafkin Njuwa da ke kauyen Rugange a karamar hukumar Yola ta kudu, jihar Adamawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya jajantawa waɗanda haɗurran suka shafa

Yayin da yake jajantawa iyalan mamatan, Shugaban ƙasa Tinubu ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata sakamakon haɗurran jiragen ruwan.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya ce:

“Shugaban ƙasa ya umurci hukumomin gwamnati daban-daban da suka hada da jami’an tsaro, masu tsaron ruwa da hukumomin kula da harkokin sufuri da su hada kai wajen gano musabbabin wadannan bala’o’i masu ban tausayi."

Kara karanta wannan

Hatsarin Kwale-Kwale: Yadda Mutum 16 Yan Gida Daya Suka Mutu a Jihar Arewa

Shugaba Tinubu ya jaddada kudirin sa na dorawa hukumomin gwamnati alhakin duk wani abu na saɓa ka’ida ko na tsaro a harkokin sufurin jiragen ruwa a ƙasar nan.

Pulse ta rahoto kakakin Tinubu na cewa:

"Tinubu ya kuma buƙaci a sake nazari kan matakan tsaro da tabbatar da bin dokokin da ake da su kan ayyukan jiragen ruwa a kasar nan."
"Shugaban ya tabbatar wa iyalai da al'ummomin da abin ya shafa cewa gwamnati zata tallafa musu kuma zata yi duk mai yiwuwa wajen hana afkuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba."

Kotun Zabe Ta Ayyana Zaben Ɗan Majalisar Tarayya A Matsayin Wanda Bai Kammalu Ba

A wani rahoton kuma Kotun zaɓen NASS mai zama a jihar Legas ta soke sakamakon zaben ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Eto Osa.

Da take yanke hukunci, Kotun ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba kuma ta umarci INEC ta shirya sabo cikin kwanaki 90.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hawaye Sun Zuba Yayin Da Kwale-Kwale Ya Sake Ajalin Mutane Da Dama Bayan Ya Kife A Cikin Ruwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262