Binciken Godwin Emefiele Ya Fallaso Abubuwan da Su ka Faru a CBN Tun 2016
- Bankin CBN ya fitar da rahoton kudin da ya batar daga shekarar 2016 har zuwa 2022 a Najeriya
- Kwamitin Jim Obazee bai gamsu da alkaluman da CBN ya fitar ba, ya na sabon bincike na musamman
- Idan Bola Tinubu ya sa hannu a takardar binciken, babban bankin kasar zai janye rahoton da ya fitar
Abuja - Watakila gwamnati ta tursasawa babban bankin Najeriya na CBN ya janye rahoton binciken kudinsa da ya fitar a watan da ya gabata.
Rahoton da aka samu daga Punch ya tabbatar da hakan ya biyo bayan alamomin tambaya da aka gani tattare da rahoton binciken kudin bankin.
Yanzu haka Bola Tinubu ya dauko Jim Obazee domin yin binciken rawar da Godwin Emefiele ya taka a tsawon lokacin da ya shafe a rike da CBN.
Aikin da IFRS tayi wa CBN
Bayan CBN, Obazee ya na binciken hukumomin gwamnatin tarayya irinsu NNPC, NIRSAL da FRC a kokarin gwamnati na yin yaki da rashin gaskiya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daga nan ne aka fara bankado babban bankin CBN ya kashe N401.75m wajen biyan cibiyar IFRS domin ta fitomasa da yadda aka bi wajen binciken kudi.
IFRS karamin kamfani ne da aka kirkiro domin horas da mutane kan ilmin akantaci sannan babu bukatar CBN su biya kudi saboda rahoton da aka fitar.
Rahoton ya kara da cewa bai halatta bankin ya mika sirrinsa ga kamfanin wajen gida ba.
Za ayi watsi da rahoton CBN?
Ganin haka ya sa kwamitin zai sa kafar wando daya da babban bankin domin janye rahoton bayanan kudin da aka tattara na shekarun 2016-2022.
Kwamitin binciken ya kuma gayyato wasu masu binciken kudin da su ka yi aikin domin yi masu tambayoyi ganin ba a yarda da alkaluman CBN ba.
Hukumar DSS za ta iya aika goron gayyata ga shugaban FRC, Mista Shuaibu Ahmed da wasu ma’aikatansa da nufin yi masu tambayoyi a kan aikinsu.
Binciken zai iya shafan hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya kan yadda su ka gudanar da ayyukansu.
Kwangilar titi a Kudancin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bada aikin gyara hanyar Amanwozuzu-Uzoagba-Eziama-Orie-Amakohia, amma an samu labari cewa aikin bai kai ko ina ba.
Mutumin Ibo ne aka kwangilar a N1.1bn, ana zargin babu abin kirki da aka yi wa titin. David Umahi ya ce 'dan kwangilar ya ba jama’ansa kunya.
Asali: Legit.ng