“Idan Lasifika Ba Zai Yi Aiki Ba, Ta Yaya Abuja Za Ta Yi Aiki”: Wike Ya Caccaki Jami’an FCTA
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi sabon gargadi ga jami'an hukumar raya birnin tarayya (FCTA)
- Wike wanda ya tsitiye su kan gazawarsu wajen samar da lasifika mai aiki a wajen wani taro, ya jaddada cewar gwamnatinsa ba za ta lamunci karbar uzurorinsu ba
- Tsohon gwamnan na Ribas ya caccaki jami'an FCTA din a bainar jama'a, yana mai cewa kada irin haka ya sake faruwa a gaba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi wa jami'an hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCTA) wankin babban bargo.
Wike ya caccaki jami'an hukumar kan gazawarsu wajen shirya taro mara tangarda yayin kaddamar da aikin gyaran wata hanya a Abuja a ranar Litinin 11 ga watan Satumba.
Ministan na jawabi ne ga jama'a a wajen taron lokacin da lasifan ya daina aiki da kyau, Channels TV ta rahoto.
"Idan ba ku son aiki, ku tattara komatsanku", Wike ga ma'aikatan FCTA
Wike ya fusata yayin da yake kokarin yin jawabi ga taron jama'a.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya dauki zafi kan ma'aikatan hukumar ta FCTA sannan ya gargade su da imma su gyara zama ko kuma su tattara su bar gwamnatin.
A cikin bidiyon da ya yadu ya ce:
"Bari na nuna rashin jin dadi na ga FCTA. Wannan abun takaici ne, kuma wannan shine dalilin da yasa babban birnin tarayya yake a inda yake. Idan ba za ku iya shirya lafika kawai ya yi aiki ba, ta yaya babban birnin tarayya zai yi aiki? Bari na gargadi wadanda abun ya shafa cewa wannan ya zamo karo na karshe da zan halarci taron jama'a, sannan na samu wannan abun kunyar, kba zai sake faruwa ba. Idan ba ku son aiki, ku tafi."
Kalli bidiyon lokacin da Wike ya fusata a kasa:
Nyesom Wike: Daga shiiga ofis, sabon ministan Abuja ya kama ayyukan tituna 135
A gefe guda, Legit.ng ta rahoto a baya cewa ministan birnin tarayya watau Abuja, Nyesom Wike ya kaddamar da ayyukan gyaran tituna 135 a garin Abuja a ranar Litinin.
Tun a ranar Asabar, Darektan yada labarai na ofishin Mai girma Minista, Anthony Ogunleye ya sanar da za a kaddamar da ayyukan a yau.
Asali: Legit.ng