Gwamna Ya Kawo Motocin Da Za Su Rika Daukar Mutane Kyauta Saboda Tsadar Fetur

Gwamna Ya Kawo Motocin Da Za Su Rika Daukar Mutane Kyauta Saboda Tsadar Fetur

  • A dalilin tashin da litar man fetur ta yi, Gwamnatin Edo ta samar da motoci domin hawa kyauta
  • Godwin Obaseki ya ce kamfanin Edo City Transport Ltd za su rika jigilar mutane duk rana a Benin
  • Gwamnatin Babagana Zulum ta kawo manyan motoci da za su rika daukar ma’aikatan jiharsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Edo – Gwamnatin jihar Edo ta kaddamar da shirin sufuri ta yadda mutanenta za su rika zirga-zirga a motoci ba tare da biyan kudi ba.

Vanguard ta ce a jiya aka kawo wannan tsari na daukar mutanen jihar Ribas a motocin kamfanin gwamnati, Edo City Transport.

Gwamna Godwin Obaseki ya amince da hakan ne a sakamakon tashin da fetur ya yi bayan gwamnati ta cire tsarin tallafin mai a Mayu.

Motocin jihar Borno
Motocin gwamnatin jihar Borno Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Yadda za ayi amfani da tsarin

Za a shafe watanni biyu ana cin moriyar wadannan motoci da za su rika jigilar mutane daga Benin zuwa sauran manyan birane.

Kara karanta wannan

A Kokarin Gyara A Harkar Ilimi, Abba Kabir Ya Dauki Mummunan Mataki Kan Wasu Shugabannin Makarantu 2 A Kano

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton ya ce motocin za su rika aiki ne tsakanin 6:30 na safe zuwa karfe 7:00 na yammacin kowace rana har na tsawon lokacin.

Gwamna ya kaddamar da motoci

Gwamna Obaseki ya yi bayani da yake jawabi wajen bude taron da aka yi a tashar ECTS.

Kwamishinan sadarwa da wayar da kan al’umma, Chris Nehikhare, ya yi kira ga mutanen Edo da yake jawabi a madadin gwamnan.

Nehikhare ya ce an kawo motocin ne saboda a saukake masu wahalar da ake ciki saboda tashin farashin fetur zuwa sama da N600.

Shugabar kamfanin Edo City Transport Ltd, Edugie Agbonlahor; ta ce dama can ana daukar daliban firamare da sakandare kyauta.

Aikin Babagana Umara Zulum a Borno

A jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da motoci 70 domin saukaka zirga-zrigar ma’aikata zuwa wuraren aikinsu.

Kara karanta wannan

Tallafi: Yayin Da Ake Halin Kunci, Matasa Sun Yi Warwason Shinkafa Kan Motoci 3 A Arewa, Bayanai Sun Fito

Rahoton FRCN ya ce Babagana Zulum ya nuna za a ware 30 daga cikin motocin su rika daukar ma’aikata da safe, a dawo da su da maraice.

Shirin kara haraji gaskiya ne?

Fadar shugaban kasa ta ce ‘Yan Najeriya su daina tunanin karin haraji da yawan canjin dokokin kudi, Bola Tinubu bai da niyyar hakan.

Gwamnati ta ce aikinta shi ne rage adadin masu biyan haraji, a ragewa mutane nauyin da ke wuyansu ba a lafto masu wasu haraji ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng