Jimami Yayin Da Kwale-Kwale Ya Sake Kifewa Da Fasinjoji Da Dama A Jihar Adamawa

Jimami Yayin Da Kwale-Kwale Ya Sake Kifewa Da Fasinjoji Da Dama A Jihar Adamawa

  • Jimami yayin da mutane su ka rasa rayukansu bayan jirgin ruwa ya nitse a jihar Adamawa
  • Mafi yawan wandanda abin ya shafa mata ne da yara da su ke dawo wa daga gona da kuma radin suna
  • Wannan na zuwa ne sa'o'i 48 bayan mutane takwas sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Yola ta Kudu

Jihar Adamawa - An sake samun hatsarin jirgin ruwa a kauyen Gurin da ke karamar hukumar Fufore na jihar Adamawa.

Lamarin ya faru a yau Litinin 11 ga watan Satumba da rana wanda mafi yawan fasinjojin mata ne da yara.

Hatsarin jirgin ruwa ya kashe mutane da dama a Adamawa
Cikin Kwanakin Nan Ana Yawan Samun Hatsarin Jirgin Ruwa A Najeriya. Hoto: Vanguard.

Yadda hatsarin jirgin ruwa ya faru a Adamawa

Rahotanni sun tabbatar da cewa mafi yawansu su na dawo wa ne daga gona yayin da wasu kuma su na dawo wa daga radin suna.

Kara karanta wannan

A Kokarin Gyara A Harkar Ilimi, Abba Kabir Ya Dauki Mummunan Mataki Kan Wasu Shugabannin Makarantu 2 A Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa kwale-kwalen katakon ya kife tare da nutsewa cikin ruwan nan take.

Wannan na zuwa ne sa'o'i 48 bayan mutane takwas sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Rugange da ke karamar hukumar Yola ta Kudu da ke jihar.

Babbar sakataren Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa (NEMA), Dakta Mohammed Sulaiman ya tabbatar da faruwar lamarin.

Martanin hukumomi kan hatsarin jirgin ruwan a Adamawa

Dakta Sulaiman ya ce lamarin ya faru ne a yau Litinin 11 ga watan Satumba da rana inda ya ce ana kan ceto mutanen da abin ya rutsa da su.

Har ila yau, dan majalisar da ke wakiltar Fufore/Gurin shi ma ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari.

Wani mai suna Mahmud wanda direba ne da ke kokarin ceto wadanda abin ya rutsa da su ya ce akwai hanyoyi da dama na kare faruwar hakan.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kuma Kai Mummunan Farmaki Da Tsakar Dare, Sun Yi Ajalin Mutane 11, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

Ya ce idan da ace fasinjojin na amfani da abubuwan kariya da duk irin wannan abu ba zai faru ba, Daily Post ta tattaro.

Ya kirayi hukumomi da su gyara hanyoyin ruwa tare da samar da kayayyakin kare lafiya don dakile faruwar hakan a gaba.

Wannan yawan hatsarin jirgin ruwa da ake samu ya fara jefa tsoro a zukatan mutane musamman lokacin damuna.

Mutane 24 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Neja

A wani labarin, wani iftila'i ya auku a jihar Neja da safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Satumba dalilin kifewar wani jirgin ruwa a jihar..

Rahotanni sun tabbatar cewa ba a san dalilin faruwar hatsarin ba da kuma yawan wadanda abin ya rutsa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.