"Asarar Kudi Ne Kawai": Fasto Ayodele Ya Yi Hasashen Abin Da Zai Faru Da Atiku, Peter Obi a Kotu

"Asarar Kudi Ne Kawai": Fasto Ayodele Ya Yi Hasashen Abin Da Zai Faru Da Atiku, Peter Obi a Kotu

  • Fasto Elijah Ayodele ya yi hasashen abin da zai faru da Atiku Abubakar da Peter Obi a kotun ƙoli
  • Shugaban na cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya bayyana cewa zuwa kotun ƙoli asarar kuɗi ne kawai ga Atiku da Obi
  • Faston ya yi iƙirarin cewa Atiku da Obi ba za su iya nasara akan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba a kotun ƙoli

Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Fasto Elijah Ayodele, ya bayyana abin da ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun Labour Party da PDP, Peter Obi da Atiku Abubakar, za su tarar a kotun ƙoli.

Fasto Ayodele ya bayyana cewa Obi da Atiku ƙuɗinsu kawai za su ɓarnatar ta hanyar zuwa kotun ƙolin saboda ba za su iya sanya wa a soke nasarar Shugaba Tinubu ba, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Bayyana Muhimmin Dalili 1 Da Yakamata Atiku/Peter Obi Su Amince Da Hukuncin Kotu

Fasto Ayodele ya yi hasashen rashin nasara ga Atiku, Obi a kotun koli
Fasto Ayodele ya ce Atiku da Peter Obi asarar kudi kawai za su yi a kotun koli Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele/Mr Peter Obi/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Asarar kuɗi ne zuwa kotun ƙoli

Babban faston ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Osho Oluwatosin, ya fitar a ranar Lahadi, 10 ga watan Satumban 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Zuwa kotun ƙoli kamar watsa naira biliyan ɗaya ne a cikin wuta. Na gaya musu Tinubu a shirye yake amma ba su saurare ni ba."
"Peter Obi da Atiku ba za su iya yin nasara a kotun ƙoli ba, su manta kawai su jira lokacin wani zaɓen. Yakamata ace sun koyi darasi yanzu ta yadda za su shirya sosai kan zaɓe na gaba mai zuwa."

Obi, Atiku ba su bi hanyar da ta dace ba

Ya ƙara da cewa ubangiji ya so ƙwace mulki daga hannun jam'iyyar All Progressives Congress (APC) amma ƴan adawa ba su bi hanyar da ta dace ba.

Kara karanta wannan

"Peter Obi Ya Kusa Zama Shugaban Kasa": Babbar Malamar Addini Ta Fadi Wani Sabon Wahayi

Fasto Ayodele ya ƙara da cewa abin da Najeriya ta ke buƙata a yanzu ba hukuncin kotun ƙoli ba ne.

"Abin da Najeriya ta ke buƙata yanzu ba hukuncin kotun ƙoli ba ne. Ƴan adawa ba su ji abin da aka gaya musu ba tun da farko. Siyasa ta wuce wasa, sai an haɗa da addu'a, jajircewa da gwagwarmaya." A cewarsa.
"Atiku da Obi ba su shiryawa zaɓen nan ba, ubangiji ya so ƙwace mulki daga jam'iyya mai mulki amma ƴan adawa ba su bi hanyar da ta dace ba."

Peter Obi Ya Aike Da Sako Ga Masoyansa

A wani labarin na daban, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya aike da saƙo ga magoya bayansa bayan ya yi rashin nasara a kotun zaɓe.

Ɗan takarar ya buƙaci magoya bayan na sa da kada su yanke ƙauna duk kuwa da koma koma bayan da ya samu a kotun zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel