Fasto Daniel Olukoya Ya Soki Fastoci Da Ke Kiran Kansu Manzanni Kan Karairayin Zabe

Fasto Daniel Olukoya Ya Soki Fastoci Da Ke Kiran Kansu Manzanni Kan Karairayin Zabe

  • Bayan hasashen da Fastoci a Najeriya su ke yi kan zabe, shahararren Fasto Daniel Olukoya ya soki irin wadannan Fastoci
  • Faston ya ce abin bakin ciki ne yadda Fastocin da ke kiran kansu manzanni su ka ci mutuncin addinin Kirista
  • Ya ce babu abin da ba su fada ba kan zabubbukan da aka gudanar a watan Faburairu amma babu abin da ya faru

Jihar Legas - Shugaban cocin Mountain of Fire and Miracle Ministries (MFM) Fasto Daniel Olukoya ya soki Fastoci masu harsashen karya a zaben 2023.

Daniel Olukoya ya ce wannan tsantsar hauka ce mutum ya ce ubangiji ya fada masa alhali bai ce masa komai ba, Legit.ng ta tattaro.

Fasto Olukoya ya soki Fastoci masu hasashen karya a zabe
Fasto Daniel Olukoya Ya Yi Martani Kan Masu Hasashen Zabe. Hoto: Daniel Olukoya.
Asali: Facebook

Meye Faston ya ce kan zabe?

Olukoya ya ce majami'a ba wurin siyasa ko kamfe ba ne na siyasa, wurin wa'azin addini ne.

Kara karanta wannan

Wani Batura Ya Canja Dala Zuwa Naira, Ya Siya Shinkafa, Wake Da Kayan Dadi Don More Rayuwa a Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Faston ya bayyana haka ne yayin huduba a cocin a jiya Lahadi 10 ga watan Satumba.

Akin Akinwale, mamba a kwamitin jam'iyyar APC a jihar Osun shi ya wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter.

Ya ce sun ci mutuncin addini kan zabe

Faston ya ce:

"Ku na ganin abin da ya faru a zaben 2023, cin mutuncin addinin Kirista ne, Fasto ya ce wannan zai ci zabe wancan ba zai ci ba.
"Idan wannan ya ci zan dawo mai ba da maganin gargajiya, idan wancan ya ci a yanke hannu na, idan wancan ya ci zabe zai mutu kafin kaza.
"Dukkan wadannan ba wanda ya faru, kuma su na kiran kansu manzanni, wannan hauka ne kawai, coci ba wurin siyasa ba ne."

Fastoci da dama a Najeriya sun bayyana cewa ba za a rantsar da shugaban kasa, Bola Tinubu ba a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Wike: Abokin Fadan Atiku Ya Yi Wa PDP Shakiyanci a Kan Shari'ar Zaben 2023

Wannan na zuwa ne bayan hukumar zabe ta bayyana Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Fasto Elijah ya gargadi Peter Obi Kan zabe

A wani labarin, A yayin da 'yan Najeriya ke zaman jiran hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe, David Elijah, shugaban cocin Glorious Mount of Possibility Church, ya gargadi Peter Obi.

Fasto David ya gargadi dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour da ya yi taka tsan-tsan da wasu na kusa da shi da masu goyon bayansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.