Kotun Sauraran Kararrakin Zabe Ta Kori Dan Majalisar Wakilai Na Jam’iyyar PDP a Jihar Imo
- An bayyana korar dan takarar majalisar wakilai ta kasa a zaben da ya gudana a Najeriya biyo bayan wasu matsaloli
- AN ruwaito cewa, za a sake zaben nan da kwanaki 90 don gano gaskiyar wanda ya ci zabe a mazabar da ke jihar Imo
- Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da sanar da sakamakon shari’ar kararrakin da aka shigar a gaban kotunan Najeriya a bana
Jihar Imo - Kotun sauraren kararrakin zaben Majalisar Dokoki ta Kasa da ta Jiha a Jihar Imo ta kori dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Ideato ta Arewa da Kudancin Jihar, Ikeagwuonu Ugochinyere na Jam’iyyar PDP, The Nation ta ruwaito.
A wani hukunci da aka yanke, gamayyar alkalai uku na kotun karkashin jagorancin mai shari’a Anthony Akpovi, sun amince da cewa Ugochinyere bai cancanci tsayawa takara a zaben ba.
Sun kafa hujja da cewa, ya fito ne daga zaben fidda gwanin da ba shi da inganci, wanda aka gudanar a wajen mazabar gabanin babban zabe.
Yaushe za a sake zaben?
Kotun ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 90 a rumfunan zabe 55, inda mai shigar da kara ya yi nasarar tabbatar da cewa ba a gudanar da zabe ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Har ila yau, ta haramtawa Ugochinyere da jam’iyyarsa ta PDP shiga zaben da aka ba da umarnin sakewa, bayan da suka karya dokar zabe ta hanyar gudanar da zaben fidda gwanin da bai inganta ba.
Sakamakon zaben baya da aka soke
Idan dai ba ku manta ba INEC ta bayyana dan takarar PDP Ugochinyere a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 13,026, rahoton Vanguard.
Yayin da dan takarar jam’iyyar LP, Chigozie, ya zo na biyu da kuri’u 5,696, wanda ya shigar da karar da APC ta dauki nauyinsa, ya zo na uku da kuri’u 2,368.
Ana ci gaba da bayyana sakamakon kararrakin da aka shigar tun bayan kammala shari’ar da ta dauki lokaci a cikin shekarar nan.
An tabbatar da zaben sanatan Legas na APC
A wani labarin kuma, kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Asabar ta tabbatar da Wasiu Eshinlokun-Sanni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Legas ta tsakiya.
Dan takarar jam’iyyar PDP Francis Gomez, ta bakin tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Joseph Daudu (SAN), ya koka kan wasu abubuwan yace jam’iyyar APC da dan takararta ba su samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba.
Ya yi zargin cewa zaben ya kasance dauke da kura-kurai da cin hanci da rashawa, inda ya nemi kotu ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Asali: Legit.ng