Soludo Ya Yabawa Tinubu Kan Ba Inyamurai Mukamai Masu Karfi Duk da Cewa Ba Su Zabe Shi Ba

Soludo Ya Yabawa Tinubu Kan Ba Inyamurai Mukamai Masu Karfi Duk da Cewa Ba Su Zabe Shi Ba

  • Gwamnan jihar Anambra ya bayyana kadan daga karamcin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi musu a yankin Kudanci
  • A cewarsa, an ba ‘yan Kudu mukamai masu kyau duk da cewa basu zabi APC ba a zaben shugaban kasan da aka yi
  • Shugaban kasa Tinubu ya nada mukamai da yawa, ciki har da na ministoci daga hawansa mulki zuwa yanzu da ake magana

Jihar Anambra - Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra, ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan yadda ya baiwa Inyamurai mukamai na siyasa masu gwabi duk da cewa ya sha kaye a jihohinsu a lokacin zabe.

Ya fadi haka ne a karshen mako yayin ziyarar ban girma da ministan ayyuka da gidaje David Umahi ya kai a jihar Anambra, inda yace ma’aikatar ayyuka a yankin Kudu maso Gabas lamari ne mai girma, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zan taimake ku: Tinubu ya mika sakon jajantawa da karfafa gwiwa ga sarkin Moroko

Ya kuma bayyana kadan daga abin da tsarin siyasa yake na samun goyon baya ko wani mukami mai karfi ba tare da wani abin tabukawa a kamfen ba.

An ba Kudu kujeru masu gwabi, cewar Soludo
Soludo ya yaba da yadda Tibubu ya karrama Kudu maso Gabas | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Jawaban Soludo kan karamcin Tinubu

Da yake jawabi, ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Idan aka yi la'akari da yawan kuri'un da muka bayar daga Kudu maso Sabas da kuma mukaman ministoci, mai yiwuwa ba mu da dalilin fara neman mukamai "masu dadi" amma shugaban kasa ya ba mu kyauta mafi kyau kuma mafi nagarta.”

Hakazalika, ya yi tsokaci ga yadda Najeriya ya kamata ta kasance kasa bai daya ga duk wani dan da ke cikinta a Kudu ko Arewacin kasar.

Ayyukan da yake roko a yi a Anambra

Gwamnan ya tunatar da tsohon gwamnan jihar Ebonyi cewa duk hanyoyin gwamnatin tarayya a jihar Anambra sun lalace, ya kuma roki gwamnatin tarayya ta gyara, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Rayuwa Juyi-Juyi: Na Taba Yin Gadi, Ilmi Ya Jawo Na Zama Shugaban Kasa - Tinubu

Soludo ya ce:

“Gwamnatin tarayya na can zaune a Abuja kuma tana kokarin bayar da kwangilolin hanyoyi a kowane lungu da sako na kasar nan.
“Gaskiyar magana, duk hanyoyin tarayya sun salwanta. A halin yanzu muna kashe kudi har Naira biliyan 20 kan hanyoyin gwamnatin tarayya.”

Wadanda aka lissafo za a ba minista

A wani labarin, manyan yan siyasa da dama da masu biyayya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da fafutukar ganin sun samu shiga jerin ministocinsa na karshe.

Kamar yadda jaridar The Sun ta rahoto, jerin sunayen da aka tattara yana cike da yan tsohuwar jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) a kudu maso yamma.

Ana ganin wani shahararran dan siyasa, Prince Dayo Adeyeye, wanda ya kafa kungiyar SWAGA a 2023 shine ya yi nasarar samun mukamin daga jihar Eikiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.