Dalibar Jami'ar Jihar Gombe Ta Halaka Jaririn Da Ta Haifa
- Wata ɗaliba a jami'ar jihar Gombe (GSU), ta jefar da jaririnta ta taga bayan ta haife shi a ranar Asabar, 9 ga watan Satumban 2023
- Ɗalibar wacce ke aji huɗu a jami'ar ta aikata wannan ɗanyen aikin ne bayan ta haifi jaririn a cikin banɗaki
- Majiya ta tabbatar da cewa ɗalibar ta haihu ne ba tare da aure wanda hakan ne ya sanya ɗaukar wannan mummunan matakin
Jihar Gombe - Wata ɗaliba ta halaka jaririn da ta kawo duniya a jami'ar jihar Gombe (GSU).
Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa ɗalibar da aikata wannan ɗanyen aikin ne a ranar Asabar, 9 ga watan Satumban 2023.
Ɗalibar wacce aka bayyana sunanta a matsayin Rahab, tana aji huɗu ne a sashin koyar da harkokin al'umma (Public Administration) na jami'ar.
Yadda ɗalibar ta halaka jaririn
Ɗalibar ta jefar da jaririn ne ta taga bayan ta haihu wanda hakan ya sanya kansa ya fashe har ya mutu, rahoton The Nation ya tabbatar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wata majiya wacce ba ta son a ambaci sunanta a jarida ta bayyana cewa ɗalibar ta haihu ne ba tare da aure ba.
Ɗalibar ta jefar da jaririn ne ta taga bayan ta haihu da misalin ƙarfe na 8:00 na safiyar ranar Asabar a ɗaya daga cikin banɗakunan ɗakin kwanan ɗalibai na jami'ar.
A cewar majiyar, bayan an gudanar da bincike an kama ɗalibar kuma aka miƙa ta a hannun hukumar jami’ar inda aka fara kai ta asibiti domin a tabbatar da koshin lafiyarta, inda daga bisani aka sada ta da mahaifan ta.
Ko da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, domin jin ta bakinsa kan lamarin, ya bayyana cewa bai samu labarin ba amma zai yi bincike domin sanin yadda lamarin yake.
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ɗalibi a makarantar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ɗalibin ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da safe misalin ƙarfe 8:00 zuwa 8:30.
Ya bayyana cewa bayan ta jefo jaririn ya mutu, nan da nan mutane suka taru suka fara kururuwa wanda hakan ne ya janyo hankalin jami'an tsaro suka zo wajen. Daga nan suka tafi da ita asibiti aka duba lafiyarta da samar mata abin da za ta ci.
Ya ce har yanzu dai hukumar makarantar ba ta fitar da wani cikakken bayani ba dangane da lamarin.
Dalibin Jami'a Ya Halaka Budurwarsa
A wani labarin na daban, wata matashi ɗalibin jami'ar Fatakwal (UNIPORT) mai shekara 24 a duniya ya shiga hannun jami'an ƴan sandan bisa zargin halaka budurwarsa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo, Muhammed Dankwara, ya shaida wa manema labarai a birnin Benin cewa mai gidan wanda ake zargin ne ya kai kara ga ƴan sanda.
Asali: Legit.ng