FG Ta Yi Alkawarin Kare 'Yan Najeriya Daga Fadawa Kangin Talauci
- Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin kare 'yan Najeriya daga fadawa kangin talauci a kasar
- Ministar ma'aikatar jin kai da walwalar jama'a, Dakta Betta Edu ita bayyana haka a jiya Juma'a
- Ta ce Tinubu ba iya dakile talauci ya shirya yi ba har ma da kare mutane daga fadawa kangin talauci a fadin kasar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa suna kokarin hana 'yan Najeriya gangarawa talauci ne ba wai dakile ta kadai ba.
Ministar jin kai da walwalar jama'a, Betta Edu ita bayyana haka a Maiduguri a jiya Juma'a 8 ga watan Satumba.
Meye gwamnatin ta ce kan talauci?
Hadimin ministar a bangaren yada labarai, Rasheed Zubair ya bayyana cewa Tinubu ya himmatu wurin yaye talauci a kasa, Concise News ta tattaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Edu wacce Gwamna Babagana Zulum ya karbi bakwancinta ta bayyana cewa Tinubu na kokarin rage yawan matsalolin da su ka shafi jama'a.
Ta kara da cewa Shugaba Tinubu ya kuma himmatu wurin dakile talauci gaba daya a kasa baki daya.
Ta ce:
"Ya na da matukar muhimmanci yadda ma'aikatar mu ta yi hadaka da gwamnatin jiha don amfana da kwarewarsu don kawo karshen matsalolin.
"Ma'aikatar karkashin jagoranci na ba dakile talauci kadai za ta yi ba, har ma da kare jama'a da gangarawa talauci."
Wane alkawari Zulum ya yi na dakile talauci?
Ta bayyanawa Gwamna Zulum cewa su na kokarin dawo da 'yan gudun hijira zuwa gidajensu nan da shekarar 2024.
A martaninshi, Zulum ya jaddawa goyon bayanshi ga Gwamnatin Tarayya wurin taimakawa a rage matsalolin al'umma, The Guardian ta tattaro.
Ya bayyana cewa da zarar an dakile talauci a kasa, rashin tsaro zai ragu inda ya ce ci gaba da ajiye 'yan gudun hijira a sansaninsu ba zai dore ba.
Legit.ng Hausa ta ji ta bakin wasu kan wannan lamari na cire mutane a talauci.
Bashir Sani, wani dan kasuwa a Gombe ya ce wannan labarin sun dade su na sauraro a kafafen ya da labarai.
Ya ce:
"Ba yau mu ka fara jin haka ba, mun dade tun gwamnatocin da su ka shude, idan za su kawo sauki ga jama'a kawai su kawo."
Muhammda Sani Adamu ya ce ai tuni ya cire rai da irin wadannan karairayi na gwamnati saboda idan an fada ba za a aikata su ba.
Wani da bai ambaci sunan sa ba ya ce wannan ai daga baya kenan, maganar talauci ai a cikinta ake tuntuni.
Edu ta bayyana tsare-tsaren Tinubu kan N-Power
A wani labarin, Dakta Betta Edu, ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci, ta ce Gwamnatin Tarayya karkashin Bola Tinubu, za ta yi wa shirin N-Power sabbin sauye-sauye.
Ministar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da hadiminta Rasheed Zubair ya fitar a ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng