Ma’aikaciyar Jinya Da Ke Karbar 20k a Najeriya Ta Yi Balaguro Zuwa Turai, Tana Karbar Miliyan 45.2
- Wata yar Najeriya ta tashi daga karbar N20,000 a matsayin ma'aikaciyar jinya a Najeriya zuwa mai karbar babban albashi duk shekara a Birtaniya
- Matashiyar ta bayyana yadda ta dunga fadi tashi a tsakanin aikin da ke kawo mata kasa da N200k kafin ta yi balaguro zuwa Turai
- Mutane da dama sun jinjinawa ma'aikaciyar jinyan da kuma hazikanci da ta nuna kan aikin tsawon shekaru
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata matashiyar budurwa yar Najeriya da ke samun albashi kadan a matsayin ma'aikaciyar jinya a Najeriya ta yi balaguro zuwa Birtaniya kuma ta samu karin albashi.
Matashiyar ta ce albashinta na farko a matsayin ma'aikaciyar jinya a Ibadan ya kasance N20k duk wata. Bayan ta rasa aikin da ake biyanta N45k yayin da take naman aiki a Lagas.
Albashin ma'aikaciyar jinya a Najeriya da Birtaniya
Ma'aikaciyar jinyar (@proudnursemj) ta zo ta samu aikin da za a dunga biyanta N75k wata a VI, amma kudin mota yana lakume babban kaso daga kudaden shiganta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta samu dan cigaba shekaru bayan nan yayin da ta samu aikin da ake biyanta 108k a VI. Wannan ya kasance lokacin da ta kusa komawa Birtaniya a 2019.
Albashin ma'aikaciyar jinya mai lasisi
Matashiyar yar Najeriyar ta bayyana cewa ta fara aiki a matsayin ma'aikaciyar jinya mai lasisi a mataki na 5 kafi aka kara mata matsayi zuwa mataki na 7 inda ta fara shiga tiyata.
Wani binciken intanet ya nuna cewa sabon shigar ma'aikaciyar jinya a mataki na 7 tana karbar £43,742 (N43,047,018.36) duk shekara. Kiran kanta a matsayin manaja, tana iya karbar albashi tsakanin £45,996 (N45,265,206.35) da £50,056 (N49,260,700.26).
Ga wallafarta a kasa:
Jama'a sun yi martani
@OXY_Medix ta ce:
"Na taya ki murna MJ.
"Ina alfahari da ke da kuma matakin da kika kai kanki...Idan da ace jajaircewa suna ne, toh da wannan zai zama sunanki na biyu. Cigaba da hawa sama yar'uwa."
@ufombachibuike ta ce:
"Ina addu'an samun karfin gwiwar bayar da labarina wata rana da kuma fadi ba tare da digon hawaye ba na taya ki murna MJ."
@SamdGreat01 ta ce:
"Rayuwa ba daidai take tafiya ba a kodayaushe. Jajircewarka da kwarewarka ne sakayyar. Yanzu kika fara hawa matakin nasara."
Yan Najeriya sun yi zanga-zanga kan yawan cajin bankuna
A wani labari na daban, mun ji cewa yan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a wasu yankuna na jihar Lagas saboda yawan cajin kudade da bankunan kasar ke yi wa jama'a.
Kamar yadda wani bidiyo da @mufasatundeednut ya wallafa a shafinsa na Instagram ya nuna, an yi zanga-zangar ne a Yaba da VI.
Asali: Legit.ng